'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an NSCDC Kwanton Bauna, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an NSCDC Kwanton Bauna, an Samu Asarar Rayuka

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi barna a jihar Edo bayan sun farmaki jami'an hukumar NSCDC
  • An kashe jami'an NSCDC wadanda suke aikin rakiyar wasu 'yan kasar waje bayan an yi musu kwanton bauna
  • 'Yan bindigan sun kuma raunata wasu jami'an tare da yin awon gaba da daya daga cikin mutanen da ake yi wa rakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Edo - 'Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe jami’an hukumar NSCDC guda takwas a jihar Edo.

'Yan bindigan sun kuma yi garkuwa da wani ɗan kasar China a harin da suka kai a garin Okpella, karamar hukumar Etsako ta Gabas ta jihar Edo.

'Yan bindiga sun kashe jami'an NSCDC a Edo
Hoton jami'an hukumar NSCDC suna atisaye Hoto: @OfficialNSCDC
Source: Twitter

'Yan bindiga sun yi wa jami'an NSCDC kwanton bauna

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa maharan sun kuma ji wa jami’an NSCDC guda huɗu da wani mutum ɗaya rauni.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane, an yi awon gaba da wasu 130 a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da suka yi rauni ana ba su kulawa a wani asibiti da ba a bayyana ba, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Jami’an na hukumar NSCDC da abin ya shafa suna aiki ne da kamfanin simintin BUA.

Lamarin ya auku ne a kusa da kofar shiga kamfanin lokacin da suke aikin rakiyar ‘yan kasar China guda biyar.

Majiyoyi sun ce maharan, waɗanda ke ɗauke da manyan makamai, sun buɗe wuta kai tsaye kan jami’an tsaron, inda suka kashe guda takwas a wurin.

Sun kuma yi garkuwa da ɗaya daga cikin ‘yan kasar China, yayin da aka ceto sauran guda huɗu ba tare da rauni ba.

'Abin da ya faru' - Jami'in NSCDC

Wani babban jami’in NSCDC a jihar Edo ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa jami’an suna kan aikin rakiyar yau da kullum ne lokacin da ‘yan bindigan suka kai hari da misalin karfe 10:00 na dare.

"An kashe jami’anmu takwas, yayin da wasu guda biyar ciki har da wani farar hula suka samu raunuka. An yi garkuwa da ɗan ƙasar China guda ɗaya, amma an ceto sauran guda huɗu ba tare da wani rauni ba."

Kara karanta wannan

Jerin kananan hukumomin Katsina da su ka rungumi sulhu da 'yan ta'adda

- Wani jami'in NSCDC

Majiyar ta kara da cewa ‘yan bindigan sun yi kwanton ɓauna ne a kofar shiga kamfanin, inda suka yi musayar wuta da jami’an NSCDC kafin su tsere da ɗaya daga cikin ‘yan kasar China zuwa cikin daji.

'Yan bindiga sun kashe jami'an NSCDC a Edo
Taswirar jihar Edo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cewar jami’in, an kaddamar da aikin hadin gwiwar jami’an tsaro don kutsawa cikin dajin, da nufin ceto mutumin da aka sace, tare da kamo waɗanda suka aikata laifin.

Kwamandan NSCDC na jihar Edo, Gbenga Agun, ya ziyarci wurin da abin ya faru da kuma jami’an da suka ji rauni a asibiti.

Da aka tuntubi mai magana da yawun NSCDC a jihar Edo, Efosa Ogbebor, ya ki yin tsokaci kan lamarin, yana mai cewa za a fitar da sanarwa daga hedikwatar NSCDC ta kasa.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kashe mutane shida bayan sun kai wasu hare-hare a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Mutane gari sun yi zazzafan artabu da 'yan bindiga

'Yan bindigan sun kai hare-haren ne a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Sabuwa ta jihar.

A yayin hare-haren, 'yan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutane wadanda yawansu ya kusa kai 200.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng