Halin da Ake Ciki a Sokoto da Fusatattun Matasa Suka Farmaki Mataimakin Gwamna
- Jami'an tsaro sun dauki mataki kan wasu da ake zargin sun farmaki mataimakin gwamnan jihar Sokoto
- Wasu fusatattun matasa ne suka kai hari kan tawagar mataimakin gwamnan a karamar hukumar Shagari
- Rahotanni sun ce wasu da bala’in ‘yan bindiga ya raba su da muhallansu ne suka tare hanya, suka kai hari kan tawagarsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Shagari, Sokoto - Wasu fusattatun matasa sun farmaki mataimakin gwamnan jihar Sokoto saboda hare-haren yan bindiga.
A kalla an kama mutum hudu bayan hari kan tawagar mataimakin gwamnan Sokoto da yake dawowa daga ziyarar jaje a Shagari.

Source: Twitter
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa mataimakin gwamnan ya kai ziyara Shagari domin jaje ga mutanen da ‘yan bindiga suka tarwatsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya damu mutanen jihar Sokoto
An gano cewa matasan sun fusata ne saboda yadda aka yi watsi da su bayan hare-haren yan bindiga da ke ci gaba da ta'azzara a yankunan.
Jihar Sokoto na daga cikin jihohin Arewa da ke fama da matsanancin rashin tsaro bayan Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma sauran jihohi.
Hakan ne ma ya sa wasu matasa ke kokarin daukar mataki da kansu tun da hukumomi ba su yin abin da ya dace kamar yadda wasu ke zargi.
Matakin da mutanen Sokoto ke dauka
Ko a kwanan nan yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a jihar Sokoto inda suka yi awon gaba da mutanen wani kauye zuwa cikin daji.
Mutanen garin da lamarin ya auku sun yi ta maza, suka fantsama cikin daji domin yin artabu da 'yan bindigan da suka kawo musu hari.
Namijin kokarin da jajirtattun mutanen garin suka yi, ya sanya sun samu nasara kan 'yan bindigan da suka zo cutar da su.

Source: Facebook
Yadda aka farmaki mataimakin gwamnan Sokoto
An tabbatar da cewa yayin da mataimakin gwamnan ke dawowa daga ziyarar ta'aziyya ne aka kai masa harin.

Kara karanta wannan
Gaba ta yi tsanani tsakanin yan bindiga, an kashe wasu jagorori 2 da suka addabi jama'a
"Yayin da yake dawowa da misalin karfe 1:00 na rana, wasu matasa sun tare tawagarsa tare da lalata wasu daga cikin motocinsa.
"Dakarun tsaro na 'Operation Fansan Yamma' sun kawo dauki inda suka yi kokarin kawo doka da oda a wurin.
"An kama mutane hudu da ake zargi kan lamarin yayin da aka tura su zuwa sashen bincike na CID domin gudanar da binciken kwa-kwaf."
- Cewar wasu majiyoyi
Majiyoyin sun kara da cewa an dawo da zaman lafiya a yankin, an kuma kara tsaro domin hana sake tashin wata fitina a gaba, Daily Post ta tabbatar.
Sokoto: Matasa sun gaji da harin 'yan bindiga
A baya, mun ba ku labarin cewa matasa sun fara fusata kan matsalar tsaro da har yanzu gwamnati ta gaza magance wa a sassan Najeriya.
Matasan yankin karamar hukumar Shagari da ke jihar Sokoto sun yi wani zama kan hare-hare da cin mutuncin da yan bindiga ke yi a yankinsu.
Sun bukaci gwamnatin jiha da ta tarayya su gaggauta daukar mataki na zahiri ba surutu ba, idan ba haka ba za su dauki makami.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
