Yadda 'Yan Bindiga Ke Karbar Haraji har N500,000 kafin a Birne Mamaci a Kabari

Yadda 'Yan Bindiga Ke Karbar Haraji har N500,000 kafin a Birne Mamaci a Kabari

  • Shugabannin al'ummomi da dama sun koka cewa yan bindiga suna kashe jama’a sannan suna tilasta musu biyan haraji
  • Wani matashi Dominic Okoli ya ce an kashe mutane sama da 25, an lalata gidaje 30, aka hana makarantu da asibitoci aiki
  • Nduka Ozor ya bayyana cewa a wasu yankunan an kashe mutum 60 ciki har da Sarki, kuma ana tilasta wa mutane biyan kuɗin birne mamata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Lamarin yan bindiga ya fara wuce gona da iri yayin da ake korafin suna karbar haraji kafin a birne mamaci.

Wasu shugabannin al’umma a Lilu da Agwa da ke jihohin Anambra da Imo ne suka yi wannan korafi.

Al'umma sun koka kan harajin yan bindiga kafin birne mamaci
Gungun yan bindiga da dakarun sojojin Najeriya. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Haraji: Yan bindiga sun taso al'umma a gaba

Shugabannin sun bayyana haka ne a yayin gabatar da rahoton 'Amnesty International' a kan kisan gilla a Kudu maso Gabas a Ikeja, Lagos, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Yadda shugaba Tinubu ke yawan nadin mukamai ya warware daga baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Al'ummomin sun koka cewa ana tilasta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu biyan kuɗin harajin birne mamata ga yan bindiga.

Sakataren fada na Lilu, Dr. Dominic Okoli, ya bayyana cewa tsakanin 2020 zuwa 2025, an kashe mutum 25 sannan an lalata gidaje fiye da 30.

Okoli ya bayyana cewa al’umma na fuskantar matsala ta kiwon lafiya, makarantu sun tsaya, kuma mahara suna karɓar kuɗi kafin a binne mamata.

Ya ce:

“Mu na son birne mamatanmu, amma kafin ka birne mamaci dole sai ka je ka nemi izini daga yan bindiga, a kuma biya su kudi.”
Jama'ar wasu yankuna sun koka kan harajin yan bindiga a yankin Imo
Taswirar jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Nawa 'yan bindiga ke karba kafin birne mamaci?

A na shi bangare, Nduka Ozor daga Agwa ya tabbatar da cewa ana tilasta biyan kuɗin birne mamata, wanda a wasu lokuta zai kai N500,000.

Ya ce an kashe mutane da dama ciki har da Sarki, ɗan uwansa, da mace mai ciki, kuma duk maharan a bayyane suke yi babu rufe fuska.

Kara karanta wannan

Rasuwar tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya ta bar baya da kura, an samu bayanai

Ya yi kira ga jami’an tsaro da shugabanni su taimaka, yayin da 'Amnesty International' ta bukaci gwamnati ta bincika kisan gilla a Kudu maso Gabas.

Rundunar ‘yan sanda a Anambra ba ta amsa tambayoyi game da lamarin ba, yayin da hare-haren suka ci gaba da ta da hankalin jama’a da masana.

A watan Yuli da Agusta, mutum 12 aka kashe a wasu al’ummomi a Imo, yayin da aka sace yara uku a Amansea, Anambra.

Rahoton ya bayyana cewa an kashe daya daga cikin yaran bayan ya ki bin umarnin masu garkuwa da shi kan ɗabi’ar da suka bukata.

'Yan bindiga sun kakabawa manoma haraji

Kun ji cewa yan bindiga sun saka rayuwar mutanen ƙauyukan Tsafe ta Yamma cikin barazana bayan lafta musu haraji mai tsoka.

Tsagerun waɗanda suke aiki a ƙarƙashin jagorancin shugabansu Danisuhu, sun sanya harajin N172m ga ƙauyuka 25 na ƙaramar hukumar Tsafe.

Sanya harajin da ƴan bindigan suka yi ya tilastawa jama'a yin ƙaura daga gidajensu saboda gudun abin da zai biyo baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.