Gwamna Ya Haramta Wa Malaman Addinin Musulunci Yin Wa'azi? Gaskiya Ta Fito

Gwamna Ya Haramta Wa Malaman Addinin Musulunci Yin Wa'azi? Gaskiya Ta Fito

  • Gwamnatin jihar Neja ta karyata labarin da ake yadawa cewa ta haramta wa malaman addini yin wa'azi ba tare da izini ba
  • Hukumar kula da harkokin addinai ta jihar Neja ta roki jama'a su rika tantance labari kafin yada shi domin gujewa yada bayanan karya
  • Shugaban hukumar, Umar Farouq Abdullahi ya ce babu dalilin da zai sa su hana malamai yin wa'azi bisa son rai, sai dai idan sun karya doka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Rahoton da ake yadawa cewa Gwamna Mohammed Umaru Bago ya haramta wa malaman musulunci da na kirista wa'azi a jihar Neja ba gaskiya ba ne.

Gwamnatin jihar Neja ta karyata rahoton, tana mai bayyana shi a matsayin karya da wasu suka kirkira domin yaudarar jama'a.

Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago.
Hoton Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago a wurin taro Hoto: Mohammed Umar Bago
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ambasada Haruna Mustapha, mai taimaka wa shugaban hukumar kula da harkokin addini na jihar Neja ya fitar, in ji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Wasu ma'aikata sun jawo wa kansu, gwamna ya kore su daga aiki nan take

Haruna Mustapha ya bayyana cewa babu wani umarni da aka taba bayarwa na hana wa’azi a jihar Neja.

Yadda aka fara jita-jitar hana wa'azi a Neja

Tun farko dai wani rahoto da ake yadawa a kafafen sada zumunta da jaridu ya nuna cewa gwamnatin Neja ta hana malamai wa'azi ba tare da izini ba.

Rahoton ya yi ikirarin cewa shugaban hukumar kula da harkokin addinai na Neja ya ce dole ne a tantance malamai kafin a ba su izinin yin wa'azi, The Cable ta kawo labarin.

Amma a sanarwar da Haruna Mustapha ya fitar, ya ce wannan labari karya ne, babu inda gwamnatin Neja ta sanya wannan doka.

Da gaske Gwamna Bago ya haramta wa'azi?

Sanarwar ta ce:

“Hankalin hukumar kula da harkokin addini ta jihar Neja ya kai ga wasu rahotanni marasa tushe da ke yawo a kafafen sada zumunta da jaridu cewa an haramta yin wa’azi a jihar.

Kara karanta wannan

An fara hayya hayya a Neja bayan hana malamai wa'azi sai da lasisi

"Wannan labari ba gaskiya ba ne, jita-jita ce ta karya da wasu suka kirkira kuma suka yada."

Shugaban hukumar harkokin addinai ta Neja, Umar Farooq Abdullahi, ya jaddada cewa hukumar ba ta da hurumin hana malamai yin wa’azi bisa son rai.

Gwamna Umaru Bago.
Hoton Mai girma Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago Hoto: @honbago
Source: Facebook

Ya ce:

“Hukumar za ta iya tsoma baki ne kawai idan aka karya ka’idojin da aka shimfiɗa. A kowane lokaci, ba mu taba fitar da wata doka ko umarni na hana wa’azi gaba ɗaya ba.”

Gwamnatin Neja ta bukaci jama’a da su yi watsi da irin waɗannan rahotanni marasa tushe tare da dogaro da sahihan majiyoyi wajen samun ingantaccen bayani.

Gwamna Bago ya sallami duka kwamishinoninsa

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Mohammed Umaru Bago ya rusa majalisar zartarwa ta jihar Neja a wani bangare na yiwa gwamnatinsa garambawul.

Hakan dai na nufin gwamnan ya sallami duka kwamishinoni da wasu manyan jami'an gwamnati da ke cikin Majalisar Zartarwa ta jihar.

Sai dai Gwamna Bago ya bar sakataren gwamnati, shugaban ma'aikatan Neja da waus manyan ma'aikata a fadar gwamnatin Neja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262