Kalaman Gwamna Dauda kan Ta'addanci Sun Jaza Masa, an 'Gano' Maƙarƙashiya da Yake Yi
- Kalaman Gwamna Dauda Lawal na Zamfara sun bar baya da ƙura yayin da yake shan suka daga wasu jama'a
- Kungiyar 'Zamfara Good Governance Network' ta soki gwamna Lawal kan cewa zai iya dakile ta'addanci a mako biyu
- Shugaban kungiyar, Murtala Abdullahi, ya ce ikirarin gwamnan abin dariya ne da wulakanci ga jami'an sojoji
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Wata kungiyar farar hula mai suna 'Zamfara Good Governance Network' ta dura kan Gwamna Dauda Lawal na Zamfara.
Kungiyar ta bukaci Gwamna Lawal ya daina sumbatu, ya mika bayanan sirri ga jami’an tsaro.

Source: Facebook
Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da Punch ta bibiya inda ta ce maganganun gwamnan suna da hatsari da kaskantar da sojoji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ikirarin Gwamnan kan matsalar tsaron Zamfara
Wannan na zuwa ne bayan ikirarin gwamnan cewa zai iya kawo karshen rashin tsaro cikin mako biyu idan aka ba shi iko kan rundunonin tsaro.
Mutane da dama sun yi ta tsokaci inda wasu ke gaskata gwamnan yayin da wasu ke zarginsa da kawo cikas a lamarin.
Kungiya ta kalubalanci kalaman Dauda Lawal
Sai dai kungiyar ta ce bai kamata hakan ya fito daga bakin gwamnan ba wanda ya yi rantsuwar kare rayuka da duniyoyi.
Sanarwar ta ce
“Ina mai tuna cewa wannan shi ne gwamnan da a yakin neman zabe ya yi alkawarin kawo karshen rashin tsaro a Zamfara.
“Yanzu kusan shekaru uku cikin mulkinsa, yana cewa zai iya shawo kan matsalar cikin watanni biyu idan yana da ikon jami’an tsaro.
“Wannan abin dariya ne, kuma abin takaici ga jaruman sojoji da ke sadaukar da rayukansu a Zamfara."
Shawarar da aka ba Gwaman Dauda Lawal
Kungiyar ta bukaci gwamna Dauda Lawal ya mika bayanai ga ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro, DSS ko manyan hafsoshin soji.
“Gwamna Lawal ya yi ikirarin sanin inda ‘yan bindiga suke, har ya ce yana iya ganin zirga-zirgarsu a wayarsa.
“Amma maimakon mika bayanin ga hukumomi, yana boyewa, yayin da ake kashe mutane da sace su kullum wannan ba komai ba ne face hadin baki da miyagu."
- Cewar shugaban kungiyar

Source: Original
Ana so a sanya dokar ta-ɓaci a Zamfara
Kungiyar ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Zamfara saboda kashe-kashe da manyan sace-sace a Kaura Namoda da Bukkuyum.
Ta kuma bukaci kungiyoyin farar hula, shugabannin addini da na al’umma su nemi gaskiya da daukar mataki kan gwamnatin jihar, Daily Post ta ruwaito.
Ya kara da cewa:
“In ba zai iya ba, to gwamnati tarayya ta karbi iko domin ceto Zamfara daga rushewar gaba daya."
Gwamna Dauda ya yi addu'a ga yan bindiga
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Dauda Lawal ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummomin da ‘yan bindiga suka kai hari a Kauran Namoda.
Dauda Lawal ya ce Allah SWT zai tona asiri ya kuma wulakanta masu daukar nauyin ‘yan bindiga, yana kira ga jama’a da su dage da addu’a.
Dauda Lawal ya yi alkawarin inganta tsaro da samar da ababen more rayuwa kamar hanyoyi, wutar lantarki da ruwa a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

