Za a Koya wa 'Yan Najeriya 2,000 Hada Motocin Lantarki da Gyaransu Kyauta
- Shirin haɗin gwiwa tsakanin YIPF da CAWIN Mobility zai bai wa matasa 2,000 damar samun horo kyauta kan kera motocin lantarki
- Shirin zai haɗa ɗalibai masu karatu a makarantu guda 1,000 da kuma sauran guda 1,000 daga sassa daban-daban na ƙasar nan
- Manufar ita ce samar da ƙwararru domin Najeriya ta shiga jerin kasashen da ke shirye wajen sabuwar fasahar motoci masu aiki da lantarki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Najeriya ta kaddamar da wani shiri na musamman domin horas da matasa 2,000 kan yadda ake gyara da kuma kera motoci masu amfani da lantarki.
Rahotanni sun nuna cewa hakan wani yunƙuri ne na sa ƙasar cikin harkokin sufuri da makamashi da duniya ke karkata zuwa gare shi.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa shirin zai gudana ne ta haɗin gwiwar YIPF da CAWIN Mobility kuma zai fara ne a ranar 20 ga wannan wata, inda za a bai wa mahalarta cikakken horo kyauta.

Kara karanta wannan
'Rashin adalci ne,' Sanata Ndume ya ce ana mayar da harin Boko Haram batun addini
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban YIPF, Tony Nwulu, ya bayyana shirin a matsayin wata dama da za ta sanya matasan Najeriya gaba wajen ci gaban fasahar sufuri na zamani.
Za a horas da matasan Najeriya kyauta
Tony Nwulu ya ce shirin zai bai wa matasa damar shiga cikin damar da ke tasowa a fannin makamashi.
A cewarsa:
“Daya daga cikin manyan ƙalubalen da ke tafe shi ne wa zai rika gyaran wadannan motocin idan suka samu matsala. Wannan shirin na da nufin cike gibin.”
Ya ce horon zai haɗa ɗalibai 1,000 da kuma mutane 1,000 a fadin Najeriya, kuma za a gudanar da shi kyauta ba tare da mahalarta sun biya komai ba.
Dalilin kawo shirin ga 'yan Najeriya
Nwulu ya kara da cewa shirin ba wai kawai zai taimaka wajen kara cinikin motoci masu lantarki ba ne, sai dai zai samar da ƙwararrun masu gyara motocin idan sun baci.
Daily Trust ta rahoto ya ce:

Kara karanta wannan
Likitoci sun yi tsayin daka kan tafiya yajin aiki, sun fadi yadda gwamnati ke muzguna masu
“Motoci ne kuma kamar kowace mota suna bukatar gyara. Idan ba mu da ƙwararru a nan gida, to za su zama an bar mu a gefe.
"Wannan shiri zai tabbatar da cewa matasan Najeriya sun zama shugabanni a Afrika a wannan ci gaba na fasaha,”

Source: Facebook
Martanin majalisar wakilan Najeriya
Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan matasa, Hon. Olamijuwonlo Alao Akala, ya ce horon zai tabbatar da cewa ba a bar Najeriya baya ba a wannan zamani.
Hon. Akala ya ce:
“A yanzu duniya ta fara sayar da motoci masu lantarki. Ba za mu iya barin Najeriya a baya ba.
Wannan shiri zai tabbatar da cewa kafin su yi yawa a kasuwar mu, mun riga mun tanadi ma’aikata da kuma kayan aiki na gyara,”
Za a yaki talauci a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta yi hadaka da China domin yaki da talauci da kyautata rayuwa.
Rahotanni sun nuna cewa ministan jin kai na Najeriya, Dr Yusuf Tanko Sununu ne ya bayyana haka bayan ganawa da Jakadan China.
Jakadan China a Najeriya ya tabbatar da cewa a shirye su ke wajen hada kai da Najeriya a shirin kawar da fatara tsakanin 'yan kasarta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng