Najeriya Ta Hada kai da China, za a Ceto Miliyoyin Talakawa daga Talauci

Najeriya Ta Hada kai da China, za a Ceto Miliyoyin Talakawa daga Talauci

  • Najeriya da kasar China sun bayyana aniyar yin haɗin gwiwa a fannin jin kai da kuma yaki da talauci
  • Jakadan China a Najeriya, Yu Dunhai, ya ziyarci Ministan Jin Kai da Rage Talauci, Dr Yusuf Tanko Sununu
  • Sun tattauna batutuwan haɗin gwiwa ciki har da harkokin abinci, ilimi, noma, tsaro da horar da ma’aikata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Gwamnatin Tarayyar Najeriya da China sun bayyana shirin yin haɗin gwiwa domin tunkarar kalubalen jin kai da rage talauci a ƙasar nan.

Wannan na zuwa ne yayin da jakadan China a Najeriya, Yu Dunhai, ya kai ziyarar ban girma ga Ministan jin kai da rage talauci, Dr. Yusuf Tanko Sununu, a ranar Alhamis 4 ga Satumba, 2025.

Ministan harkokin jin kai, Dr Yusuf Sununu da jakadan China a Najeriya
Ministan harkokin jin kai, Dr Yusuf Sununu da jakadan China a Najeriya. Hoto: @FMINONigeria
Source: Twitter

Legit ta rahoto cewa ma'aikatar yada labarai ta kasa ce ta fitar da sanarwar a wani sako da ta wallafa a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Abinci: Kano, Gombe, jihohin Arewa 11 sun samu tallafin Amurka na ₦49.686bn

A yayin ganawar, Dr. Sununu ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar matsaloli da dama irin su ƙarancin abinci mai gina jiki ga yara, matsalar ‘yan gudun hijira da sauran kalubale na jin kai.

Ministan ya kara da cewa Najeriya za ta amfana matuƙa daga gogewar da China ta samu wajen yaki da talauci.

China: Za a yaki talauci a Najeriya

Sununu ya ce za a mayar da hankali kan samar da mafita na dindindin ga matsalar talauci da jin kai, horar da ma’aikata, koyon sana’o’i don habaka tattalin arziki.

Haka kuma ya bayyana cewa Najeriya za ta koyi dabarun China wajen samar da taimakon gaggawa ga al’ummomi masu rauni.

Ya kuma jaddada muhimmancin shirin “Skill to Wealth” wanda zai taimaka wa matasa da mata wajen samun dogaro da kai ta hanyar sana’o’i da kasuwanci.

Lokacin da shugaba Tinubu ya ziyarci kasar China
Lokacin da shugaba Tinubu ya ziyarci kasar China. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Kalubalen da China ta shawo kansu

A nasa jawabin, jakadan China ya bayyana cewa ƙasarsa ta shafe shekaru tana fama da yunwa da talauci, amma cikin shekaru kadan, ta samu nasarar cire miliyoyin mutane daga kangin talauci.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan bindiga bayan an yi gumurzu a Katsina

Ma'aikatar yada labarai ta wallafa cewa Yu Dunhai ya kara da cewa hakan ya samu ne ta hanyar zuba jari a noma, abinci, masana’antu, ilimi da tsaro.

Ya ce Najeriya da China suna da abubuwa da dama da suka yi kama, musamman yawan jama’a, don haka haɗin gwiwar zai taimaka wajen samar da mafita ta gari ga matsalolin yau da kullum.

Jakadan ya tabbatar da cewa ofishin jakadancin China a Najeriya zai ba da goyon baya don tabbatar da nasarar wannan haɗin gwiwa.

Za a koya wa matasa 100,000 sana'a

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar shirin NASAP na koyar da sana'o'i.

Rahotanni sun bayyana cewa shirin zai taimaka wajen koya wa matasa 100,000 sana'o'in da suke da alaka da gini a Najeriya.

Legit ta rahoto cewa za a fara shirin ne a jihohi kadan a 2025 kafin daga bisani a kaddamar da shi a dukkan jihohin kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng