Yadda Shugaba Tinubu ke Yawan Naɗin Muƙamai Ya Warware daga baya

Yadda Shugaba Tinubu ke Yawan Naɗin Muƙamai Ya Warware daga baya

A watannin baya-bayan nan, an ga yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke yin canji ga manyan nade-naden gwamnati, a wasu lokutan, a cikin kwanaki kaɗan bayan sanar da su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Wadannan sauye sauye sun fara jan hankalin jama'a, musamman ganin cewa akan sanar da soke nadi a cikin 'yan kwanaki ba tare da an fiar da cikakken bayanin dalilin hakan ba.

Shugaban kasa na yawan amai yana lashe wa a nadin mukamai
Hoton Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Yawancin wadanda aka nada ba su ma gama samun damar shiga ofis ba kafin a cire su, kamar yadda za a karanta a wannan rahoto.

Yadda Tinubu ya canja shugabannin NTA

The Cable ta wallafa cewa a ranar 20 ga Agusta, shugaban kasa ya sanar da nadin Rotimi Pedro, wani mai gogewa a fannin yada labarai sama da shekaru 20, a matsayin babban daraktan NTA.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi yadda manufofin Tinubu su ka ceto albashin ma'aikata a jihohi 27

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce matakin zai karfafa kafar yada labaran ta kasa domin hadin kai da kuma karfafa manufofin diflomasiyya.

Shugaban kasa, ya dawo da Shugabannin NTA
Hoton Shugaban Kasa, Tinubu yana rubutu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A jawabin da ya fitar, Pedro ya bayyana cewa burinsa shi ne ceto wannan gidan talabijin daga lalacewa ta hanyar amfani da fasaha, da jan hankalin masu kallo.

Haka nan, Stella Din-Jacob, tsohuwar shugabar labarai a TVC, ta bayyana farin cikinta da ta samu mukamin Shugabar sashen yada labarai a NTA.

Sai dai cikin makonni biyu kacal, shugaban kasa ya janye nadin nata, na Pedro da na Karimah Bello da aka nada a matsayin Shugabar sashen kasuwanci.

Shugaban kasar ya dawo da tsofaffin shugabannin da suka riga sun ke rike da mukaman, ba tare da sanar da kowa dalilin rushe wadancan da ya nada ba.

Tinubu ya soke nadin FCC da NDDC

A cikin watan Agusta, 2025, shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi nadi mai cike da rudani a hukumar FCC ta kasa, inda ya sabunta nadin Muheeba Dankaka a matsayin shugabar hukumar.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya

Shugaban ya soke nadin da aka yi shi da 6:35 na yamma, sai kuma ya sauke ta ya naɗa tsohuwar ‘yar majalisa, Ayo Hulayat Omidiran, 10:44 na dare.

Shugaba Tinubu ya canja nadin da ya yi a FCC
Hoton Muheeba Dankaka, Bola Tinubu da Ayo Hulayat Omidiran Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

A shekarar 2024, shugaban kasa Tinubu ya nada Asu Okang, ɗan jam’iyyar PDP, a matsayin memba a hukumar raya yankin Neja-Delta (NDDC). Wannan lamari ya tayar da ƙura a wasu wurare, inda wasu ƴan jam’iyyar APC suka taru a fadar gwamnati dake Kala a, jihar Kuros Riba, domin nuna rashin jin daɗinsu. Daga baya, Tinubu ya sauya Okang da Orok Otuk Duke, wannan yana cikin lashe aman da shugaban na Najeriya ya yi a ofis.

Bola Tinubu ya janye nadi a CBN

A CBN, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya janye nadin Ruby Onwudiwe saboda goyon bayan da ta yi wa jam’iyyar Labour a zaben 2023, aka maye gurbinta da Melvin Ayogu.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun shaida wa shugaban kasa cewa bai kamata ya naɗa ta a matsayin mamban majalisar gudanarwa ta CBN ba.

Wadannan kiraye-kiragen ƙusoshin APC, ya sa Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta jingine batun naɗin Onwudiwe.

Kara karanta wannan

Farashin Dala: Bincike ya karyata ikirarin Tinubu kan farfado da darajar Naira

Yadda Tinubu ya canja Kwamishinonin INEC

A ranar 18 ga Maris, shugaban kasa Tinubu ya bukaci majalisar dattawa da ta janye nadin Mohammad Ngoshe (Borno) da Owede Kosioma Eli (Bayelsa) a matsayin kwamishinonin zabe na reshen Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Daily Post ta wallafa cewa an yi wannan canji ne a cikin kwanaki shida kacal bayan shugaban kasa ya gabatar da sunayensu a matsayin REC.

A maimakon haka, an sake tabbatar da Umar Mukhtar, wanda ke kan mukami a Borno, domin wa’adi na biyu, yayin da aka nada Johnson Alalibo Silnikiem a matsayin REC na Bayelsa.

Tinubu ya bayyana cewa wannan sauyi ya zama dole ne bayan ya yanke shawarar sabunta wa’adin Mukhtar.

Tinubu ya canja tunani a FERMA, UBEC

A ranar 13 ga Oktoba, 2023, an nada Ibrahim Kashim Imam mai shekara 24 a matsayin shugaban kwamitin hukumar kula da gyaran manyan hanyoyi ta ƙasa (FERMA).

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun cimma matsaya kan rashin tsaro, sun sanar da Shugaba Tinubu

Nadinsa ya jawo cece-kuce nan take, inda aka fara bayyana damuwa game da shekarunsa da kuma ƙwarewarsa.

A wancan lokacin, Imam na aiki ne a matsayin mataimaki ga ministan ayyuka, David Umahi.

Bayan kwana biyu kacal, shugaban kasa ya janye nadin nasa. Ba a bayar da wani dalili ba kan janye wannan mukami.

Tinubu ya janye nadin Shugaban FERMA
Hoton Bola Ahmed Tinubu da Ibrahim Kashim Imam Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Imam Mohammed
Source: Facebook

A ranar 11 ga Maris, shugaban kasa Tinubu ya nada Idris Olorunnimbe a matsayin shugaban kwamitin hukumar UBEC.

Sai dai a watan Yuli, an janye nadin nasa, aka maye gurbinsa da Tanko Umaru Al-Makura, tsohon gwamnan jihar Nasarawa.

Bayan wata guda, Tinubu ya sake nada Olorunnimbe a matsayin shugaban hukumar NCC mai kula da harkokin sadarwa.

Yadda Tinubu ya canja Shetty

Daya daga cikin farkon sauye-sauyen nade-naden da suka jawo cece-kuce a gwamnatin Tinubu shi ne janye nadin Maryam Shetty a matsayin minista.

Shetty ta gamu da babban takaici lokacin da ta isa majalisar tarayya domin tantancewa, inda a kofa aka sanar da ita cewa an janye sunanta.

Tinubu ya canja Maryam Shetty da ta hannun daman Ganduje
Maryam Shetty, Abdullahi Ganduje Hoto: Maryam Shetty/Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Source: Facebook

Tana daga cikin ministocin 37 da shugaban kasa ya tura zuwa majalisar dattawa domin tantancewa a cikin watanni uku na farko na mulkinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci

Shugaba Tinubu ya kori shugabar NCCC

A baya, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami shugabar farko ta hukumar kula da sauyin yanayi ta ƙasa (NCCC), Dr. Nkiruka Madueke.

A sanarwar da fadar Shugaban Kasa ta fitar a ranar Alhamis, 31 ga watan Yuli 2025, ta ce an nada Mrs. Omotenioye Majekodunmi a matsayin sabuwar shugabar hukumar.

An bayyana Majekodunmi a matsayin ƙwararriyar lauya a fannin muhalli da kuma masaniya kan tafiyar da kuɗi da suka shafi sauyin yanayi na shekaru 17.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng