Kano: Ciyaman Ta Sake Jawowa Abba Kabir Magana, Yan Sanda Sun Gayyace Ta

Kano: Ciyaman Ta Sake Jawowa Abba Kabir Magana, Yan Sanda Sun Gayyace Ta

  • Rundunar ‘yan sandan reshen jihar Kano ta gayyaci shugabar karamar hukuma kan zargin cin zarafi
  • Yan sanda sun gayyaci Sa’adatu Salisu, bayan zargin umartar jami’inta su kai hari kan ma’aikatan masana’anta
  • Rahotanni sun nuna an kai kan ma'aikatan, inda aka ce ta dawo da yan daba sama da 200 da makamai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wata shugabar karamar hukuma a jihar Kano ta jawo maganganu bayan zargin ta da cin zarafin wasu ma'aikata.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta gayyaci shugabar karamar hukumar Tudunwada, Sa’adatu Salisu domin amsa tambayoyi.

Yan sanda sun gayyaci shugabar karamar hukuma a Kano
Kakakin rundunar yan sanda a Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa da Hon. Sa'adatu Salisu.
Source: Facebook

Dalilin gayyatar da 'yan sandan Kano suka yi

Rahoton Daily Nigerian ya ce an gayyaci Sa'adatu ne bayan zargin kai hari kan ma’aikatan wata masana’anta a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun bayyana cewa ma’aikatan 'Tasarrufi General Enterprise' sun kai ƙara kan shugabar ALGON saboda umartar jami’inta su kai musu hari.

Kara karanta wannan

El Rufai ya fusata bayan 'yan sanda sun hana taron ADC a Kaduna

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Abdullahi Kiyawa, ya ce an fara bincike, inda aka gayyaci dukkan masu hannu ciki, ciki har da shugabar karamar hukumar.

"An kawo korafin shugaban kungiyar ALGON, kuma an gayyaci dukan shaidu da wacce ake zargi kan abin da ya faru."

Ma’aikata sun zargi shugabar ALGON da jagorantar wasu dauke da makamai, tare da umartar jami’inta ya harbe su, abin da ya jawo raunuka masu yawa, Premium Times ta ruwaito.

Manajan kamfanin, Suyudi Umar, ya bayyana cewa a ranar 28 ga Agustan 2025, Sa'adatu ta kai hari bayan takaddama da injiniyan aikin ginin hanya.

Ya ce duk da injiniyan ya nuna musu cewa masana’antar ba ta cikin yankin, Sa'adatu ta nace cewa tana iya tilasta musu barin wurin.

Ya ƙara da cewa daga baya ta dawo da wasu fiye da 200 dauke da makamai masu hatsari, inda suka farma ma’aikatan kamfanin nasa.

"Wannan shi ne karo na hudu da Sa'adatu take zuwa kamfanina, ta nace cewa sai mun bar wannan wurin."

- Cewar Umar yayin da yake kuka

Yan sanda na bincike kan zargin shugabar karamar hukuma a Kano
Mai magana da yawun rundunar yan sanda a Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa.
Source: Facebook

Korafin ma'aikata kan shugabar karamar hukumar

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tsagin Wike ya kafa sharuddan samun sulhu a jam'iyyar

Wani ma’aikaci, Mustapha Bashir, ya ce ya ji Sa'adatu na umartar jami’inta ya harbe manajan, kafin harsashi ya same shi a hannu.

Har ila yau, wani ma’aikaci, Khalifa Suyudi, ya ce ya samu karaya a hannu bayan kokarin kare shugaban kamfanin daga kai musu hari.

Ya bayyana cewa kamfanin yana waje da yankin da ake aikin hanya, amma duk da haka shugabar ALGON ta dage da tilasta musu barin wurin.

Mr Suyudi ya ce sun kai rahoto ga rundunar ‘yan sanda domin neman adalci kan lamarin inda ya ce ba a iya samun ta ta wayar salula.

Kwamishinan Abba Kabir ya yi murabus

Kun ji cewa Kwamishinan sufuri na Kano, Ibrahim Namadi, ya miƙa takardar ajiye aiki daga mukaminsa ga gwamnatin jihar.

Wannan na zuwa bayan an gudanar da bincike kan rawar da ya taka a belin dilan ƙwaya, Suleiman Danwawu.

Duk da haka, Ibrahim Namadi ya kafe kan cewa bai aikata laifin komai ba a kan zargin da aka yi masa wajen belin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.