El Rufai Ya Fusata bayan 'Yan Sanda Sun Hana Taron ADC a Kaduna

El Rufai Ya Fusata bayan 'Yan Sanda Sun Hana Taron ADC a Kaduna

  • Shugabannin jam'iyyar ADC na yankin Arewa maso Yamma sun so gudanar da wani taro a jihar Kaduna
  • Sai dai, taron bai yiwu ba bayan rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kawo cikas kafin a fara gudanar da shi
  • Nasir El-Rufai ya fito ya yi maganganu masu kaushi kan matakin da 'yan sanda suka dauka na hana yin zaman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya caccaki jami'an 'yan sanda kan hana wani taron shugabannin jam'iyyar ADC.

Nasir El-Rufai ya bayyana matuƙar rashin jin daɗinsa kan umarnin ‘yan sanda na dakatar da taron na shugabannin ADC.

El-Rufai ya caccaki 'yan sandan Kaduna
Hoton Nasir El-Rufai a wajen wani taron jam'iyyar ADC Hoto: @IU_Wakilii
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a gidansa da ke Kaduna ranar Alhamis, 4 ga watan Satumban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasir El-Rufai ya soki 'yan sanda

Kara karanta wannan

Biyan 'yan bindiga kudi: Baba-Ahmed ya yi wa El Rufai raddi mai zafi

Tsohon gwamnan ya nace cewa matakin da 'yan sandan suka dauka ya sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulki.

El-Rufai ya bayyana cewa taron an shirya shi ne domin shugabannin ADC na Arewa maso Yamma, su yi jaje ga ‘ya’yan jam’iyyar bisa harin da ake zargin ‘yan daba sun kai musu a ranar Asabar da ta gabata.

"Shirin shi ne shugabannin ADC na Arewa maso Yamma su zo Kaduna domin yi mana jaje bisa abin da ya faru ranar Asabar."
"Kuma za mu gudanar da wannan taro a ofishinmu. Sai kwamishinan ‘yan sanda ya rubuto mana cewa ba za mu iya yin taron a jihar ba."

- Nasir El-Rufai

"Yan sanda sun wuce gona da iri" - El Rufai

El-Rufai ya zargi ‘yan sanda da yin amfani da iko fiye da kima, inda ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya samo umarnin kotu da ya hana taron ba tare da an mika shi yadda ya dace ga wadanda abin ya shafa ba.

"Ya san abin da ya rubuta ya sabawa kundin tsarin mulki. Da safe, ya gayyaci mataimakin shugaban jam’iyya na kasa mai kula da Arewa maso Yamma."

Kara karanta wannan

Baba Ahmed ya fadi abin da ya kamata a yi wa El Rufai kan zargin ba 'yan bindiga kudi

"Ya ɗaga wata takarda yana ikirarin cewa sun samo umarnin kotu da ya hana mu gudanar da taron. Mu dai ba mu ga umarnin kotun ba."
"Ba a mika mana shi kamar yadda doka ta tanada ba. Ko da kuwa akwai umarnin kotu, akwai hanyar doka ta mika shi ga wanda abin ya shafa, kuma ba a yi hakan ba."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya ragargaji 'yan sanda
Hoton tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Wace shawara shugabannin ADC suka yanke?

Sai dai ya nuna cewa shugabannin jam’iyyar sun yanke shawarar girmama matsayar kwamishinan ‘yan sandan, duk da abin da ya kira rashin bin ka’ida.

"A matsayinmu na shugabanni masu kishin kasa, muna da damar zuwa mu gudanar da taronmu. Babu wanda zai iya hana mu, muna da 'yancin hakan a kundin tsarin mulki."
"Amma mun yanke shawara cewa duk da cewa ba mu ga wannan umarnin ba, mun gaskata kwamishinan ‘yan sanda. Domin ba mu yi imanin cewa kwamishinan ‘yan sanda zai yi karya ba."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya kara da cewa dalilin da ya sa suka gudanar da taron manema labarai a gidansa, shi ne don guje wa samun rikici da jami’an tsaro, inda ya nuna cewa tsawon shekara 15 bai zauna a gidan ba, saboda ana gyare-gyare a cikinsa.

Kara karanta wannan

"Na yi nadama": Tsohon hadimin El Rufai ya kwance masa zani a kasuwa

Kwankwaso ya soki El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon APC a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ragargaji Malam Nasir El-Rufai.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana cewa take-taken El-Rufai sun nuna cewa so yake ya tunzura mutanen Arewa kan Mai girma Bola Tinubu.

Sai dai, jigon na jam'iyyar APC ya bayyana cewa tsohon gwamnan na Kaduna ba zai yi nasara ba, domin 'yan Arewa ba wawaye ba ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng