Gaba Ta Yi Tsanani tsakanin Yan Bindiga, An Kashe Wasu Jagorori 2 da Suka Addabi Jama'a
- An rage mugun iri yayin da wasu yan bindiga suka yi wa manyan hatsabiban 'yan ta'adda kofar rago a jihar Zamfara
- Rahoto ya nuna cewa an kashe jagororin dabar yan bindiga biyu, Kachalla Bingil da Kachalla Mai Hidima a yankin karamar hukumar Maru
- Wasu majiyoyi sun bayyana yadda hatsabiban yan ta'addan suka gamu da ajali lokacin da suka fito zagayen kauyuka a yankin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Rikici tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga ya kara rage mugun iri a yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe fitattun jagororin yan bindiga guda biyu, Kachalla Mai Hidima da Kachalla Bingil, a wani harin kwanton-bauna da abokan gaba suka shirya musu.

Source: Original
Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ya tabbatar da hakan a shafinsa na X yau Alhamis.

Kara karanta wannan
Al'umma sun samu sauƙi, ƴan bindiga sun hallaka rikakken ɗan ta'adda da yaransa 4
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe jagororin yan bindiga 2 a Zamfara
Bayanan da aka tattara sun nuna cewa lamarin ya faru ne a tsakanin hanyar Mai Kogo zuwa Mai Aya Aya, da ke yankin Dansadau a karamar hukumar Maru.
Wata majiya ta ce yan bindiga da ba a tantance ko su waye ba ne suka kai harin, inda suka bude musu wuta tare da mutanensu, suka kuma kashe su nan take.
“Harin kwantan bauna ya rutsa da Kachalla Mai Hidima da Kachalla Bingil a yayin da suka fito yawo tsakanin kauyuka.
"Ana kyautata zaton mutuwarsu tana da nasaba da tsohuwar gaba tsakanin ƙungiyoyin ‘yan bindiga da ke aiki a dajin Dansadau,” in ji wani daga cikin majiyoyi.
Kachalla Mai Hidima ya yi aiki da Dogo Gide
Kachalla Mai Hidima, ya yi aiki ƙarƙashin shahararren jagoran ‘yan bindiga, Dogo Gide, daga baya ya balle ya kafa tasa ƙungiyar ta’addanci.
An ce ya kafa babban sansani a gabashin Gidan Fulani Mai Kudi, kusa da kauyen Hannu Tara a yankin Dansadau.
Kashe waɗannan manyan kwamandojin biyu ya nuna irin rabuwar kawuna da tsananin gaba da ke tsakanin ƙungiyoyin ‘yan bindiga a Zamfara.

Source: Facebook
Me ke haddasa gaba tsakanin yan bindiga?
Rahoto ya nuna cewa galibin kungiyoyin yan bindigar na fada da juna domin samun iko da yankuna, garkuwa da mutane da kuma haramtattun hanyoyin samun kuɗi irin su satar shanu da kakaba haraji.
“Wannan wani ɓangare ne na rikicin cikin gida da ke yawaita tsakanin ‘yan bindiga musamman a Maru, Anka da Shinkafi, inda hare-haren sojoji suka ruguza haɗin kansu,” in ji wata majiya.
Yankin Dansadau na daya daga cikin wuraren da rikicin ‘yan bindiga ya fi tsananta a Zamfara, inda ya zama sansani da mafakar ƙungiyoyin yan bindiga da dama.
Ado Aliero ya kashe mayakansa 7 a Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa hatsabibin jagoran ‘yan bindiga, Ado Aleiro, ya kashe wasu daga cikin mayakansa a jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa dan ta'addan ya sheke mayakansa guda bakwai a kauyukan Takulawa, Turba, Bamamu da kuma yankin dajin Yamma.
Majiyoyi sun ce Ado Aleiro ya zargi mutanensa da yin garkuwa da mutane ba tare da amincewarsa ba a kan hanyar Gusau–Yankara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

