Ado Aleiro: Jagoran 'Yan Bindiga Ya Kashe Mayakansa a Zamfara, an Ji Dalili
- Rigima ta kunno kai a sansanin tantirin jagoran 'yan bindiga, Ado Aleiro, wanda yake ta'addancinsa a Zamfara da wasu jihohi makwabta
- Hatsabibin dan bindigan ya bindige wasu daga cikin mayakansa bayan zargi ya shiga a tsakaninsa da su
- Ado Aleiro ya dade da shiga cikin jerin 'yan ta'addan da hukumomi suke nema saboda yadda yake gudanar da ayyukan ta'addancinsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Shahararren hatsabibin jagoran ‘yan bindiga, Ado Aleiro, ya kashe wasu daga cikin mayakansa a jihar Zamfara.
Ado Aleiro ya kashe mayakan ne guda bakwai a wasu sassan jihar Zamfara, bayan da ya zargesu da cin amana.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ado Aleiro ya hukunta mayakansa
Rahotanni sun nuna cewa kisan ya faru ne a kauyukan Takulawa, Turba, Bamamu da kuma yankin dajin Yamma.

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya
Majiyoyi sun ce Ado Aleiro ya zargi mutanensa da yin garkuwa da mutane ba tare da amincewarsa ba a kan hanyar Gusau–Yankara.
Sun bayyana cewa ya dauki abin da suka yi a matsayin barazana ga ikonsa da harkokinsa.
"Da kansa ya kashe mutum bakwai bayan ya tabbatar cewa su ne ke da alhakin satar fasinjoji kwanan nan a kan babbar hanyar."
"Ya ji tsoron cewa ayyukansu na jawo hankalin jami’an tsaro sosai."
- Wata majiya
Kisan gillan ya haifar da tsoro da rashin kwanciyar hankali a tsakanin sauran mabiyansa, wadanda suke ganin wannan a matsayin alamar rashin yarda da ke karuwa a cikin sansanin.
An dade ana zargin Ado Aleiro, wanda gwamnatin tarayya ta ayyana a matsayin babban dan ta’adda da ake nema, da kitsa garkuwa da mutane.
Ana zarginsa kashe-kashe da kuma satar shanu a sassan Zamfara, Katsina da wani bangare na jihar Sokoto.
Haka kuma, jagoran na ‘yan bindiga yana tattaunawa da kwamitin gwamnatin tarayya kan batun zaman lafiya domin kawo karshen tashin hankali a Arewa maso Yamma.

Source: Facebook
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- Gwamna ya gaji da hare hare, ya roki Allah game da masu daukar nauyin ta'addanci
- Yadda 'yan bindiga suka shirya kwanton bauna a Zamfara, an kashe jami'an tsaro
- Nasara daga Allah: Sojoji sun babbake yan bindiga fiye da 100 a Zamfara, an yada hotuna
- Rikici ya kaure tsakanin Dogo Gide da hatsabibin dan bindiga, an kashe wasu
- 'Yan bindiga sun titsiye Sarki a dajin Zamfara, ya amsa tambayoyi masu zafi
- Ana batun sulhu da Bello Turji, ƴan bindiga sun taso garuruwa 35 a jihar Zamfara
Gwamnan Zamfara ya koka kan 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya nuna damuwa kan ayyukan 'yan bindiga a jiharsa.
Gwamnan ya bayyana cewa yana zubar da hawaye saboda ta'addancin 'yan bindiga sakamakon bai da wani abu da zai iya yi a kai.
Hakazalika, ya bayyana cewa yana da masaniya kan wuraren da shugabannin 'yan bindiga suke buya, kuma ko fita suka yi zai iya sani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
