Shugaba Tinubu Ya Tafi Hutun Shekarar 2025, Ya Lula zuwa Kasashe 2 a Nahiyar Turai

Shugaba Tinubu Ya Tafi Hutun Shekarar 2025, Ya Lula zuwa Kasashe 2 a Nahiyar Turai

  • Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya dauki hutun kwanaki 10 na aiki daga cikin hutunsa na shekarar 2025
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce Tinubu zai yi hutu ne a tsakanin kasashen Faransa da Birtaniya da ke nahiyar Turai
  • Manyan kusoshin gwamnatin Najeriya sun raka Tinubu har zuwa filin jirgin sama, inda daga nan zai lula zuwa kasar da ya tsara zai fara zuwa hutu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya yau Alhamis, 4 ga watan Satumba, 2025 domin tafiya hutun kwanaki 10 a nahiyar Turai.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa wannan hutu da Bola Tinubu ya dauka na daga cikin hutunsa na aiki na shekarar 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Farashin Dala: Bincike ya karyata ikirarin Tinubu kan farfado da darajar Naira

Shugaba Bola Tinubu.
Hoton Shugaba Bola Tinubu yana daga hannu kafin shiga jirgin sama Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X yau Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai shafe kwanaki 10 a Turai

Onanuga ya bayyana cewa Bola Tinubu zai yi wannan hutu na kwanaki 10 a tsakanin kasashen Faransa da kuma Birtaniya da ke nahiyar Turai.

Sanarwar ta ce:

"Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja yau, 4 ga Satumba, domin fara hutun aiki a Turai, a matsayin wani ɓangare na hutun shekara ta 2025.
Hutun zai ɗauki tsawon kwanaki 10 na zuwa ofis. Shugaba Tinubu zai yi wannan hutun nasa tsakanin kasashen Faransa da Birtaniya, sannan daga nan ya dawo gida Najeriya."

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaban kasa Tinubu ya dawo daga tafiyar diflomasiyya zuwa kasashen Japan da Brazil, inda ya shafe kwanaki 12 kafin dawowa gida.

Shugaba Bola Tinubu ya fice daga Najeriya

Kara karanta wannan

Masoyan Buhari sun dauki matsaya kan wanda za su marawa baya a zaben 2027

A wani bidiyo da Tribune Nigeria ta wallafa, Shugaba Tinubu ya kama hanyar tafiyar hutunsa a kasashen Turai kamar yadda aka tsara yau Alhamis.

Faifan bidiyo ya nuna yadda manyan kusoshin gwamnatin tarayya suka raka Tinubu har zuwa filin jirgin sama a Abuja, daga nan ya tashi zuwa kasar waje.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton Tinubu lokacin da zai bar Najeriya zuwa nahiyar Turai Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jiga-jigan da suka raka Shugaba Tinubu zuwa filin jirgi sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.

Sauran su ne Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, Babajide Sanwo-Olu na Legas, Ministan kudi, Wale Edun da Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Atiku Bagudu.

Tinubu ya yi magana kan harjin kasar Amurka

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa matakin kakaba haraji da Donald Trump na Amurka ya dauka kan Najeriya ba abin damuwa ba ne.

Bola Tinubu ya yi ikirarin cewa Najeriya ba tsoron duk wani haraji da Donald Trump zai latfa domin tattalin arzikin kasar ya bunkasa kuma ya fara zama da gindinsa.

Tun a watan Agusta ne shugaban Amurka ya kara harajin kayan Najeriya da wasu kasashen Afirka da kaso 15%, lamarin da ya kawo cikas wajen fitar da fetur da dizal.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262