An Zo wajen: Gwamna Dauda Ya Yi Fallasa kan Matsalar 'Yan Bindiga a Zamfara
- Gwamnan jihar Zamfara ya fito ya yi magana kan matsalolin da ke kawo cikas a yakin da ake yi da 'yan bindiga
- Dauda Lawal ya bayyana cewa an kasa kawo karshen matsalar ne saboda abubuwan da suka fi karfin ikonsa
- Gwamnan ya nuna cewa duk da matsalolin da ake samu, yana bakin kokarinsa wajen ganin ya sauke nauyin da ke kansa na kare mutanen Zamfara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi magana kan matsalar 'yan bindiga da ake fama da ita.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa yana sane da ainihin wuraren da manyan shugabannin ‘yan bindigan da ke addabar jihar suke.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ambato gwamnan na cewa ba shi da ikon daukar mataki ne saboda ba shi ne ke da iko kan hukumomin tsaro ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Dauda ya tabo batun 'yan bindiga
Gwamna Dauda Lawal ya koka kan yadda yaki da 'yan bindiga yake kwan gaba kwan baya a jihar.
Ya bayyana cewa duk da sanin motsin ‘yan bindiga, an kasa shawo kana matsalar ne saboda shugabannin tsaro a Zamfara suna karɓar umarni ne kawai daga Abuja.
Gwamnan ya bayyana cewa yana da masaniya kan duk inda shugabannin 'yan bindiga suke a jihar, amma ba zai iya yi musu komai ba.
Ya nuna cewa ko fita suka yi zai sani amma ba yadda ya iya da su tun bai da iko kan hukumomin tsaro.
Gwamnan ya bayyana cewa hakan ya kan sanya ya zubar da hawaye, saboda ga matsala yana gani amma bai da ikon kawo karshenta, rahoton The Punch ya tabbatar.
“Na rantse da Allah Maɗaukaki, duk inda shugaban ‘yan bindiga yake a cikin Zamfara, na sani, kuma idan ya fita, na sani."
- Gwamna Dauda Lawal
Gwamna Dauda ya bada misali kan yadda ‘yan bindiga suka taba kai hari a karamar hukumar Shinkafi, amma jami’an tsaro a jihar suka ki tunkararsu saboda ba su samu izini daga Abuja ba.
"Akwai lokacin da ‘yan bindiga suka kutsa Shinkafi, aka sanar da jami’an tsaro, amma suka ki fita saboda kawai ba a basu umarni daga Abuja ba."
- Gwamna Dauda Lawal

Source: Facebook
Wane mataki Gwamna Dauda ke dauka?
Ya jaddada cewa gwamnatinsa ta yi duk mai yiwuwa don tallafa wa hukumomin tsaro duk da cewa ba shi da ikon shugabanci a kansu kai tsaye.
"Ina yin hakan ne duk da cewa ba ni da iko a kan hukumomin tsaro, amma saboda nauyin da ke kaina na kare rayuka da dukiyoyin jama’ar Zamfara."
- Gwamna Dauda Lawal
Mutanen gari sun yi fito na fito da 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mutanen gari a jihar Sokoto sun yi arangama da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan
Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci
Mutanen sun nuna jarumta inda suka shiga cikin daji suka fafata da 'yan bindiga bayan sun yi awon gaba da wasu bayin Allah.
Artabun da suka yi, ya sanya sun samu nasarar ceto mutanen da aka sace tare da hallaka wasu daga cikin 'yan bindigan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

