Trump: Amurka Ta Sake Fitar da Gargadi game da Rashin Tsaro a Najeriya
- Gwamnatin Amurka ta kare matakin da ta dauka na soke bizar ’yan Najeriya da dama, tana mai cewa tsaron kasa ne ya tilasta hakan
- Rahotanni sun bayyana cewa dalibai, ’yan kasuwa da masu yawan tafiye-tafiye daga Najeriya sun shiga damuwa kan soke bizar da aka yi
- Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da gargadi ga ’yan kasar da ke zaune a Najeriya kan ziyartar wasu wurare na musamman
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa matakin da ta dauka na soke bizar wasu ’yan Najeriya da aka riga aka basu, ba ya da nasaba da son zuciya.
Amurka ta ce an dauki matakin ne a shirin tsauraran matakan tsaro da suka zama dole domin kare iyakokinta da lafiyar ’yan kasarta.

Source: Getty Images
Vanguard ta wallafa cewa sanarwar ta zo ne a lokacin da ofishin jakadancin Amurka ya sake fitar da wani gargadi ga ’yan kasar da ke Najeriya da su guji tafiya zuwa wasu wurare a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin ya ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya da dama, musamman dalibai, ’yan kasuwa da iyalai da aka sokewa bizar ba tare da wani gargadi ba.
Matakin soke biza da martanin Amurka
Tsohon kakakin NNPC, Femi Soneye, ne ya fara bayyana korafin cewa dubban ’yan Najeriya sun samu wasiƙar gaggawa cewa su da su mika fasfo ɗinsu domin a soke bizar.
Amurka ta ce matakin ya yi daidai da tanadin dokar INA ta kasar da ta baiwa ministan harkokin waje da jakada ikon soke biza a kowane lokaci idan aka samu alamar rashin cancanta.
Punch ta wallafa cewa mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka ya shaida cewa ana cigaba soke biza sosai domin tabbatar da tsaron Amurka da kare al’ummarta.
Gargadi ga ’yan kasar Amurka a Najeriya
Baya ga batun bizar, ofishin jakadancin Amurka ya sake jaddada gargadinsa ga ’yan kasar da ke Najeriya da su guji tafiya zuwa wuraren gwamnati da sansanonin soji saboda barazanar tsaro.
Sanarwar ta bukaci su guji shiga taron jama’a masu yawa, tare da tsara dabarun tsaron kai domin kauce wa fadawa cikin hatsari.
Hakan ya zo ne bayan wasu gargadi makamantan wannan da aka saba yi a baya, musamman bayan fashewar bam a kusa da a barikin Mogadishu a hanyar Mararaba-Nyanya a Mayu.
A watan Maris ma ta umarci ’yan kasarta da su guji zuwa babban masallacin Abuja, sannan a Yuni ta jaddada gargadi kan kada a yi tafiya marar dalili zuwa wuraren gwamnati da sansanonin soji.

Source: Facebook
Barazanar tsaro da matakan kariya
A cewar sanarwar, Amurka ta dauki wannan mataki ne saboda irin rikice-rikicen da ake samu a kusa da muhimman wuraren tsaro a Najeriya a ’yan watannin nan.
Ofishin ya ce ma’aikatan jakadanci da ’yan kasar suna da damar zuwa irin wadannan wurare ne kawai idan an tilasta musu ta hanyar aikin gwamnati.
Amurka ta yi kira da a kara sa ido da yin taka-tsantsan a Najeriya, tare da tabbatar da cewa ba za a yi watsi da kariyar lafiyar ’yan kasarta ba.
Amurka ta tallafawa Najeriya da abinci
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta tallafa wa Najeriya da abincin da ya kusa kai Naira biliyan 50.
Rahotanni sun bayyana cewa za a raba kayan abincin ne a jihohi 13 na Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Amurka ta samar da tallafin ne ga mutane kusan miliyan 1 da suka shiga garari sakamakon matsalar rashin tsaro a yankunan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


