Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Bama Bama kan 'Yan Boko Haram, an Soye Miyagu

Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Bama Bama kan 'Yan Boko Haram, an Soye Miyagu

  • 'Yan ta'addan Boko Haram masu tayar da kayar baya sun kwashi kashinsu a hannu, bayan dakarun sojoji sun farmake su a jihar Borno
  • Jiragen yakin rundunar sojojin saman Najeriya sun kai samame a maboyar 'yan ta'addan da ke cikin dajin Sambisa
  • Farmakin da sojojin suka kai, ya sanya an kashe mayaka da kwamandojin kungiyar ta'addancin wadda ta yi kaurin suna wajen kai hare-hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Rundunar sojojin saman Najeriya ta samu nasarar hallaka 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

Rundunar sojojin saman ta ce ta kashe sama da ‘yan ta’adda 15 a wani harin bama-bamai da ta kai a maboyarsu da ke dajin Sambisa, jihar Borno.

Sojojin sama sun kashe 'yan Boko Haram a Borno
Hoton hafsan rundunar sojojin Najeriya, Air Marshal Hasan Abubakar da jiragen yaki Hoto: @NigAirforce
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Alhamis, 4 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan bindiga bayan an yi gumurzu a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojojin sama sun ragargaji 'yan Boko Haram

Rundunar ta bayyana cewa an gudanar da samamen ne a ranar Laraba, 3 ga watan Satumban 2025.

A cewarsa, an kai harin ne kan wani sansani da ke yammacin Zuwa, wanda bayanan leken asiri da kuma sa ido suka gano a matsayin mafakar mayaka da kuma kwamandojin kungiyar.

Ya ce mayakan da kwamandojin na da alaka da hare-haren baya-bayan nan da aka kai a yankin Bitta da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno,, rahoton jarodar The Punch ua tabbatar.

An tarwatsa maboyar 'yan ta'adda

Ehimen Ejodame ya ce samamen ya lalata gine-ginen da ‘yan ta’addan ke amfani da su, tare da raunana karfin ayyukansu.

"Rundunar sojojin saman Najeriya, ta hannun sashen sojojin sama karkashin rundunar hadin guiwa ta Arewa-Maso-Gabas (Operation Hadin Kai), ta sake nuna kwarewa da kuma jajircewarta wajen yaki da ta’addanci."
"A ranar 3 ga Satumba, 2025, wani shirin luguden bama-bamai da aka tsara da kyau ya tarwatsa sabon sansanin ‘yan ta’adda da aka gano a yammacin Zuwa, cikin dajin Sambisa."

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi barin wuta, an kashe 'yan ta'adda, an kwato kayan hada bama bamai

"Bisa sahihan bayanan leken asiri da kuma tabbatarwa ta hanyar sa ido, wannan aikin ya kai hari kan maboyar da ke dauke da mayaka da kwamandojin da ke da alhakin hare-haren baya-bayan nan a yankin Bitta."
"Harin ya yi mummunan tasiri, inda ya hallaka fiye da ‘yan ta’adda 15 tare da rusa muhimman gine-ginen da suke dogara da su wajen gudanar da ayyukansu."

- Air Commodore Ehimen Ejodame

Sojojin sama sun hallaka mayakan Boko Haram a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya
Source: Original

Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yanma sun samu galaba kan 'yan bindiga a jihar Katsina.

Sojojin sun tarwatsa wasu 'yan bindiga da suka yi yunkurin yin awon gaba da wasu matafiya a.kan hanyar Funtua zuwa Gusau.

Dakarun sojojin sun samu nasarar fattatakar 'yan bindigan zuwa cikin daji tare da ceto mutanen da suka yi yunkurin tasa keyarsu da karfi da yaji zuwa cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng