Ba Imani: Mahaifiya Ta Daure Jaririyar da Ta Haifa, Ta Birne Ta da Rai a Dajin Kebbi
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta cafke wata mata mai shekara 20 da haihuwa da zargin birne jaririyarta da rai a daji
- Wani manomi ne ya gano wurin da aka birne jaririyar, inda aka tono ta kuma nan take aka garzaya da ita asibiti a Kamba
- Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bello Sani ya ce rundunarsa ba za ta lamunci cin zarafi ko keta hakkin yara a Kebbi ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi – Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta sanar da cafke wata mata mai suna Maryam Atiku, ‘yar shekara 20, bisa zargin birne jaririyarta da rai bayan haihuwa.
Lamarin ya faru ne a unguwar Nasarawa da ke cikin karamar hukumar Dandi, jihar Kebbi, ranar 25 ga watan Yuni, 2025.

Kara karanta wannan
Likitoci sun yi tsayin daka kan tafiya yajin aiki, sun fadi yadda gwamnati ke muzguna masu

Source: Original
The Cable ta rahoto cewa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa bayan haihuwa, Maryam ta dauki jaririyar da ta haifa ta birne.
Yadda uwa ta birne jaririya da rai
'Yan sanda sun bayyana cewa ta daure wuyanta da zani sannan ta rufe bakinta, kafin daga bisani ta kai ta daji inda ta tona rami ta birne ta da rai.
Rahotanni sun bayyana cewa, da misalin karfe 12:30 na rana a ranar 26 ga Yuni, wani manomi Kabiru Muhammad, da ke aiki a gonarsa kusa da kauyen Malam Yaro ya lura da ramin.
Bayan haka ne ya kira sauran mazauna yankin suka zo, suka kuma tono jaririyar da aka birne a ramin.
Lamarin ya dauki hankalin al’umma, inda aka yi gaggawar kai ta asibitin gwamnati na Kamba kuma likitoci sun tabbatar da cewa jaririyar ba ta rasu ba.
Wani mataki 'yan sanda suka dauka?
Da rundunar ‘yan sanda ta samu rahoton, tawagar jami’an sashen binciken manyan laifuffuka (SCID) daga Birnin Kebbi suka shiga cikin lamarin.
Nan take aka kama Maryam Atiku, inda ta amsa aikata laifin a lokacin da ake fara yi mata tambayoyi.
Jami’an tsaro sun ce bincike zai ci gaba domin tabbatar da hujjoji tare da gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala gudanar da cikakken bincike.
Martanin kwamishinan ‘yan sandan Kebbi
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kebbi, Bello Sani, ya bayyana cewa rundunar ta dage wajen yakar duk wani nau’i na cin zarafi da kuma tashin hankali da ake yi wa yara da mata a jihar.
Ya yi kira ga iyaye, masu kula da yara da kuma shugabannin al’umma da su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu na kare hakkin yara.

Source: Facebook
Ya kuma gargade su da kada su bari matsin tattalin arziki ko wasu kalubale su zama dalilin yin irin wannan mummunar dabi’a.
An kai wa Abubakar Malami hari a Kebbi
A wani rahoton, kun ji cewa wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun kai wa tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami hari.
Rahotanni sun nuna cewa Abubakar Malami SAN bai samu rauni ba kai tsaye, sai dai an ruguza wasu daga cikin motocin da ke raka shi.
Tsohon ministan ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya a siyasar jihar Kebbi, kuma za su yi duk mai yiwuwa wajen kare kansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

