Hotuna: 'Yan sanda sun damke mutumin da ya birne jikansa da rai

Hotuna: 'Yan sanda sun damke mutumin da ya birne jikansa da rai

- Bawada Audu mai shekaru 50 a duniya ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Bauchi

- Ana zarginsa da laifin birne jinjirin jikansa da rai a bayan gidansa har ya mutu

- An gano cewa diyarsa mai shekaru 17 ce ta haifesa bayan cikin shegen da ta dauka a shekarar nan

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta damke wani mutum mai suna Bawada Audi mai shekaru 50 a duniya, a kan kashe jaririn jikansa a Rimin Ziyam da ke karamar hukumar Toro ta jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Ahmed Wakili, wanda ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, 19 ga watan Satumba, ya ce bayan diyar wanda ake zargin mai shekaru 17 ta haihu, ya kwace jaririn inda ya birnesa.

Hotuna: 'Yan sanda sun damke mutumin da ya birne jikansa da rai
Hotuna: 'Yan sanda sun damke mutumin da ya birne jikansa da rai. Hoto daga LIB
Source: Twitter

Bawada Audu ya kwace jaririn diyarsa mai suna Hafsat bayan haihuwar da tayi sannan ya birnesa da ransa a bayan gidanshi.

"A ranar 16 ga watan Satumban 2020 wurin karfe 8 na dare, rundunar hadin guiwa tsakanin 'yan sanda da masu rajin kare hakkin dan Adam sun kawo wata budurwa.

"Yarinyar mai shekaru 17 a duniya da ke zama a Rimin Zayam a karamar hukumar Toro ta Bauchi ta ce mahaifinta ya kwace mata jinjirinta bayan ta haihu sannan ya birnesa da ransa," takardar tace.

Bayan samun rahoton, an hako jinjirin kuma an gaggauta mika shi babban asibitin yankin inda aka tabbatar da cewa ya rasu, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Hotuna: 'Yan sanda sun damke mutumin da ya birne jikansa da rai
Hotuna: 'Yan sanda sun damke mutumin da ya birne jikansa da rai. Hoto daga LIB
Source: Twitter

Kakakin rundunar 'yan sanda ya kara da cewa, "Bugu da kari, Hafsat ta sanar da cewa wani Danjuma Malam Uba da ke gidansu ya yi mata fyade a 2020, amma ya yi batan dabo.

"An bai wa dagacin kauyen gawar jinjirin yayin da aka damke wanda ake zargi kuma ya amsa laifinsa."

KU KARANTA: Buhari ya tura wakilai Zaria, sun samu halartar jana'izar Sarki Shehu Idris

Hotuna: 'Yan sanda sun damke mutumin da ya birne jikansa da rai
Hotuna: 'Yan sanda sun damke mutumin da ya birne jikansa da rai. Hoto daga LIB
Source: Twitter

KU KARANTA: El-Rufai ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya sanar da lokacin jana'iza

A wani labari na daban, wani bene ya rushe a sa'o'in farko na ranar Talata inda aka rasa rayukan mutum biyu kuma 'yan gida daya a Gwammaja 'Yan kosai, karamar hukumar Dala ta jihar Kano.

An gano cewa, mutum takwas duk a gida dayan sun samu miyagun raunika bayan sun kasa fitowa daga ginin da ya fadi.

Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano, Sa'adu Muhammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Vanguard. Ya ce Abdullahi Anas da Abdulmalik Anas sun riga mu gidan gaskiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel