Likitoci Sun Yi Tsayin Daka kan Tafiya Yajin Aiki, Sun Fadi Yadda Gwamnati ke Muzguna Masu
- Likitocin masu neman kware wa sun yi barazanar shiga yajin aiki na kasa baki ɗaya daga 10 ga Satumba idan gwamnati ta gaza biyan bukatunsu
- Kungiyar NARD ta ce sama da likitoci 2,000 ba su karɓi kuɗin horon shekarar 2025 ba yayin da wa’adin rajista zai ƙare ranar 5 ga watan Satumba
- Shugaban kungiyar, Dr. Tope Osundara, ya gargadi cewa rashin biyan hakkokin zai haifar da rugujewar tsarin kiwon lafiya a Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD) ta sake jaddada kudirinta na fara yajin aiki a fadin kasar ranar 10 ga Satumba.
Ta ce babu abin da zai hana ta tafiya yajin aikin idan gwamnatin tarayya da hukumomin da abin ya shafa suka kasa biyan bukatunsu.

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya

Source: Facebook
Shugaban kungiyar, Dr. Tope Osundara, ne ya bayyana haka a wata hira da ta kebanta ga jaridar Punch a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar likitoci ta gana da gwamnati
Dr. Tope Osundara ya kara da bayyana cewa kungiyarsu ta gana da gwamnatin tarayya a farkon mako amma ba a kai ga cimma matsayar da ta dace ba.
A baya-bayan nan, kungiyar ta bai wa gwamnati wa’adin kwana 10 da ta gaggauta magance matsalolin, idan ba haka ba za su tsunduma yajin aikin.

Source: Facebook
NARD ta soki gwamnatin tarayya bisa kin cika alkawuran da ta dauka, daga ciki har da kin biyan kuɗin horon shekarar 2025 ga likitoci.
Haka kuma ta yi zargin gwamnati ta ki biyan albashin watanni biyar da aka kara masu a bisa tsarin CONMESS, da kuma kuɗin kayan aiki na shekarar 2024.
Yadda gwamnati ta waiwayi likitoci
Shugaban kungiyar ya ce bayan matsin lambar kungiyoyi, gwamnati ta kafa kwamiti na tattaunawar hadin gwiwa a bangaren lafiya kusan makonni uku da suka gabata.
Dr. Osundara ya ce:
“Wa’adin kwana 10 yana tafiya. Har yanzu babu wani martani daga gwamnati. Abin takaici ne. Likitoci na cikin bacin rai, kuma fargabana shi ne kada tsarin kiwon lafiyar kasar ya rushe gaba ɗaya.”
Shugaban NARD ya kara da cewa fiye da likitoci 2,000 a sassan Najeriya daban-daban ba su samu kudin horon shekarar 2025 ba, kuma wa’adin rajista zai ƙare ranar Juma’a, 5 ga Satumba.
Ya ce:
“An biya wasu likitoci, wasu kuma ba a biya su ba. Wannan abu ya fusata jama’a. Likitoci da dama daga asibitocin koyarwa na Kalaba, Fatakwal, Uyo, Maiduguri da sauran wurare ba su samu kudin ba."
Wasu likitoci sun tsunduma yajin aiki
A baya, mun wallafa cewa kungiyar likitoci masu neman kwarewa ARD a asibitin koyarwa na jami’ar LAUTECH da ke Ogbomoso, jihar Oyo, ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
Kungiyar ta ce ta dauki matakin ne bayan dogon jinkiri da rashin magance ƙorafe-ƙorafen da suka daɗe suna yi ga gwamnati da shugabancin asibitin domin inganta rayuwarsu da aikinsu.
An rufe kofar shiga asibitin LAUTECH a Ogbomoso yayin da likitocin suka dakatar da aiki, lamarin da ya haifar da cunkoso ga marasa lafiya da ke neman agaji da ma’aikata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
