'Zai Koma Legas,' Ministan Buhari Ya Yi wa Tinubu Barazanar Faduwa a 2027

'Zai Koma Legas,' Ministan Buhari Ya Yi wa Tinubu Barazanar Faduwa a 2027

  • Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya ce Bola Tinubu wa’adi ɗaya kacal zai yi ya koma Legas
  • Dalung ya ce gazawar APC da PDP wajen cika burin ‘yan ƙasa ta buɗe ƙofa ga sabuwar jam’iyya hadaka ta ADC
  • Ya ƙara da cewa jam'iyyar ADC na gina sabuwar tafiya da za ta iya girgiza siyasar Najeriya a zaben shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da cewa zai iya komawa Legas a shekarar 2027 bayan wa’adinsa na farko.

Dalung, wanda babban jigo ne a jam’iyyar ADC, ya nuna kwarin gwiwa da cewa haɗin kan jam’iyyun adawa na iya dakile nasarar Tinubu a babban zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya 'tabbatar' da tazarcen Tinubu, ya ce a jira 2027

Shugaba Tinubu tare da Dalung
Shugaba Bola Tinubu tare da Dalung. Hoto: Bayo Onanuga|Solomon Dalung
Source: Facebook

Jaridar Tribune ta wallafa cewa Dalung ya ce ADC za ta ba mutane mamaki a zaben shekarar 2027 mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa gazawar manyan jam’iyyun APC da PDP wajen cika alƙawarin da suka yi wa ‘yan Najeriya ya buɗe ƙofa ga sabuwar tafiya wacce ADC ke jagoranta.

'Tinubu zai iya yin wa’adi 1 tal,' Dalung

A cewarsa, rashin ingancin tafiyar da gwamnati da tsadar rayuwa na daga cikin dalilan da ka iya tilasta Tinubu barin mulki bayan shekara huɗu kacal.

“Lokaci ya yi da zai gane cewa ya kamata ya fara shirin komawa Legas nan da 29 ga Mayu, 2027,”

- In ji shi.

Dalung ya ce talakawa sun gaji da matsalar tsaro, tattalin arzikin da ke tabarbarewa da kuma rashin shugabanci nagari. Wannan, a cewarsa, zai sa al’umma neman sauyi a 2027.

Martanin Dalung ga Tinubu kan ADC

Dalung ya yi watsi da kalaman da Shugaba Tinubu ya taba yi na cewa ADC sansanin ‘yan siyasa ne masu gudun hijira.

Kara karanta wannan

APC ta kare salon mulkin Tinubu yayin da shugabannin siyasa a Arewa ke koka wa

Ya jaddada cewa jam’iyyar tana kara karfi a fagen siyasa, tare da samun sababbin mambobi da goyon baya daga sassa daban-daban na ƙasa.

Ya ce ADC ba karamar jam’iyyar ba ce da za a raina, domin tana shirye-shiryen fitowa da ƴan takara masu inganci da za su iya kalubalantar jam'iyya mai mulki.

Shirye-shiryen ADC a fagen siyasa

Kodayake bai bayyana dabarun da za su yi ba, tsohon ministan ya ce jam’iyyar ta na ci gaba da tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki daga kowane yanki na ƙasar.

A cewarsa, wannan tsari zai tabbatar da cewa ADC za ta samar da ƴan takarar da za su iya samun amincewar jama’a, tare da yin tasiri a babban zaben 2027.

Dalung ya fadawa tashar Arise cewa:

"Muna gina wata tafiya da za ta iya ba kowa mamaki, ciki har da masu shakku kan tafiyarmu,”
El-Rufa'i, Atiku da wasu 'yan ADC a Abuja
El-Rufa'i, Atiku da wasu 'yan ADC a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Bincike ya karyata ikirarin Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa a ranar Laraba shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ya farfado da darajar Naira.

Kara karanta wannan

2027: Wike ya kyale Jonathan, ya fadi mutum 1 da zai rusa PDP idan ya samu takara

Ya bayyana haka ne yayin da ya ce ya samu farashin Dala a kan N1,900 a lokacin da ya hawu mulki a 2023.

Sai dai wani bincike da Legit Hausa ta yi ya gano cewa abin da shugaban kasar ya fada game da farashin ba gaskiya ba ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng