"Ba Laifin Tinubu ba ne," Dan Majalisa daga Kano Ya Yi Magana kan Matsalar Tsaron Arewa

"Ba Laifin Tinubu ba ne," Dan Majalisa daga Kano Ya Yi Magana kan Matsalar Tsaron Arewa

  • Dan Majalisar Wakilai daga Kano, Hon. Abdulmumini Jibrin ya ce bai kamata a dorawa Bola Tinubu laifin matsalar tsaron Arewa ba
  • Jibrin da aka fi sani da Kofa, wanda jigo ne a jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa Tinubu ya tara yan adawa a Arewa da Kudancin Najeriya
  • Babban 'dan siyasar ya ce duk da haka ba ya tunanin akwai abin da zai dakatar da shugaban kasa daga tazarce a babban zaben 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Yayin da ake da ake fama da matsalar tsaro a Arewacin Najeirya, Hon. Abdulmomini Jibrin ya yi ikirarin cewa ba laifin Shugaba Bola Tinubu ba ne.

Ɗan majalisar mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya karyata ikirarin cewa Tinubu ya kamata a ɗora wa alhakin tabarbarewar tsaro a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda shugaba Tinubu ke yawan nadin mukamai ya warware daga baya

Abdulmumini Kofa da Tinubu.
Hoton Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @Abdulabmj
Source: Twitter

Hon. Jibrin Kofa, wanda jigo ne a jam’iyyar NNPP, ya bayyana haka ne a ranar Laraba a shirin siyasa na tashar Channels tv mai suna Politics Today.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkaluma sun nuna cewa an kashe dubban mutane tare da sace sama da mutum 10,000 daga watan Mayu, 2023 zuwa yanzu.

Matsalar tsaron da ake fama da ita a Arewa

A rahoton da Amnesty Internation ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce matsalar tsaron Arewa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 10,217 cikin shekaru biyu da zuwan sabuwar gwamnati a Najeriya.

Ta lissafi jihohin da lamarin tsaron ya fi kamari kamar Benuwai, Filato, Katsina, Sakkwato, Zamfara, da Kebbi.

Wannan yasa manyan Arewa suka nemi shugaban kasa ya tashi tsaye wajen magance wannan matsala da ke kara tabarbarewa.

'Dan Majalisar ya ce ba laifin Tinubu ba ne

Da aka tambaye shi kan wannan matsala ta tsaro da Arewa ke fama da ita, dan Majalisar Kiru da Bebeji ya ce bai kamata a dora laifi gaba daya kan Shugaba Tinubu ba.

Kara karanta wannan

2027: Makusancin Kwankwaso ya hango wa Tinubu matsala idan aka yi watsi da Kashim

“Dorawa Shugaba Bola Tinubu laifin rashin tsaro a Arewa ko na Najeriya gaba ɗaya ba daidai ba ne. Mu faɗa wa kanmu gaskiya,” in ji shi.
Abdulmumini Kofa.
Hoton dan Majalisa mai wakiltar Kiru da Bebeji, Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa Hoto: Abdulmumini Jibrin
Source: Facebook

Abdulmumini wanda ya dade yana tare da shugaban ƙasa, ya ce akwai masu adawa da Tinubu a kowane yanki na ƙasar nan, ba Arewa kaɗai ba.

"Eh, gaskiya akwai mutanen Arewa da ke son ganin ya sauka. Haka nan akwai a Kudu da ke son haka. Amma kuma akwai waɗanda suke son ya ci gaba da mulki."

Duk da haka, Jibrin Kofa ya nuna kwarin gwiwa cewa Tinubu zai samu nasarar lashe zaɓe karo na biyu a 2027, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Wani matashi daga daya daga cikin yankunan da ake fama da matsalar tsaro a Katsina, Sulaiman Tukur ya ce akwai laifin shugabanni a halin da jama'a ke ciki.

Da yake tattaunawa da wakilin Legit Hausa, ya ce babu wanda zai dora wa shugaban kasa laifin kawo matsalar gaba daya amma rashin magance ta gazawarsa ce.

Matashin ya ce:

"Wannan kalamai na Kofa ba su dace ba, dan bai san halin da jama'a ke ciki ba ne, bamu barci, kullum a tsaye a cikin daji muke kwana domin tsare iyalanmu.

Kara karanta wannan

2027: Dan Kwankwasiyya ya raba gardama kan batun 'yan Arewa ba sa tare sa Tinubu

"Na yarda ba Tinubu ya kawo matsalar ba, amma rashin magance ta fa? Wa ke da hakkin tsare rayuka da dukiyoyin al'umma? Muna kara kira ga gwamnati ta yi abin da ya dace."

Kofa ya ce babu hadin kai a Arewa

A wani labarin, kun ji cewa Hon. Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu bai damu da yunkurin taron dangi da Arewa ke shirin yi masa a 2027 ba.

'Dan Majalisar Wakilan ya ce Tinubu ba zai damu da duk wani yunkuri da yan siyasar Arewa ke yi ba saboda ya san ba su da hadin kai.

Kofa ya kuma jaddada cewa ya kamata yankin Kudu ya kammala shekaru takwas bayan wa’adin mulki biyu na marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262