Dakarun Sojoji Sun Samu Nasara kan 'Yan Bindiga bayan an Yi Gumurzu a Katsina
- Sojojin Najeriya na ci gaba da kara kaimi wajen magance matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a sassa daban-daban na kasar nan
- A kokarin da suke yi na samar da tsaro, sojojin sun yi wani artabu mai zafi da miyagun 'yan bindiga a jihar Zamfara
- Dakarun sojojin sun ragargaji 'yan bindiga wadanda suka shirya wani mugun nufi kan matafiyan da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yanma sun dakile harin 'yan bindiga a jihar Katsina.
Dakarun sojojin tare da hadin gwiwar 'yan sanda sun yi nasarar dakile wani yunkurin garkuwa da mutane da ‘yan bindiga suka yi a kan hanyar Funtua–Gusau da ke jihar Katsina.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne kimanin karfe 3:00 na rana a kusa da kwanar Kwankiro da ke kauyen Kanon Haki, a karamar hukumar Faskari.
'Yan bindigan dai sun yi wa wasu motoci guda hudu kwanton bauna da nufin sace mutanen da ke cikinsu.
Motocin da aka nufa da harin sun hada da wata kirar tipper Mercedes mai launin baki, motar bas kirar Toyota mai kujeru 18 mallakar Kano Line mai launin kore.
Sauran sun hada da mota kirar Toyota Hilux mai launin fari, da kuma motar Sharon mai launin toka.
Sojoji Operation Fansan Yanma sun kai dauki
Daukin gaggawa da dakarun rundunar Operation Fansan Yanma suka kai, ya sanya aka yi musayar wuta da 'yan bindigan.
Artabun da aka yi ya tilastawa ‘yan bindigan tserewa ba tare da sun yi garkuwa da ko fasinja guda daya ba.
"An tabbatar da cewa dukkanin fasinjojin suna nan, sai dai mutane 13 sun samu raunuka daban-daban, kuma an garzaya da su babban asibitin Funtua domin samun kulawar likitoci."
- Wata majiya

Source: Original
Artabun wanda ya karfafa tsaro sosai a manyan hanyoyin jihar, ya karawa matafiya kwarin gwiwa, inda ya nuna tasirin hadin kai tsakanin sojoji da hukumomin tsaro wajen yaki da ‘yan bindiga.
Hukumomi sun tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin bin sawun maharan da suka tsere domin cafke su.
Karanta wasu labaran game da sojoji
- Dakarun sojoji sun samu nasara bayan fafatawa da 'yan bindiga a Zamfara
- An kwashi gawar 'yan bindiga a buhu bayan sojoji sun kashe 'yan ta'adda 50
- Sojoji sun yi barin wuta, an kashe 'yan ta'adda, an kwato kayan hada bama bamai
'Yan bindiga sun sace basarake a Kogi
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makami sun yi awon gaba da wani basarake a jihar Kogi.
'Yan bindigan sun yi awon gaba da Hakimin Bagaji Odo a karamar hukumar Omala ta jihar Kogi, David Wada, lokacin da yake kan hanyar komawa gida bayan ya halarci wani taro.
Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta ba da tabbacin cewa ta tura jami'ai don ganin cewa sun kubutar da basaraken.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

