Kwana Ya Kare: Tsohon Dan Takarar Gwamna Ya Rasu a cikin Gidansa a Najeriya
- Jihar Ondo ta rasa daya daga cikin manyan 'yan siyasar da suka yi takarar gwamna a zaben 2024 wanda APC ta samu nasara
- Otunba Bamidele Akingboye, wanda ya nemi zama gwamnan Ondo a inuwar jam'iyyar SDP ya riga mu gidan gaskiya yau Laraba
- Marigayin yana rike da sarauta kuma ya kasance dan kasuwa mai taimako kafin Allah ya karbi ransa da safiyar Laraba a gidansa na Legas
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Tsohon dan takarar gwamna a jihar Ondo karkashin inuwar jam'iyyar SDP, Otunba Bamidele Akingboye ya riga mu gidan gaskiya.
Otunba Bamidele Akingboye, wanda ya fafata a zaben gwamnan Ondo na 2024 da ya gabata, ya mutu yana da shekaru 60 a duniya.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da aka wallafa a shafin Marigayi Akingboye na Facebook mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Oyeniyi Iwakun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon dan takarar gwamnan SDP ya rasu
Sanarwar ta tabbatar da cewa Akingboye ya rasu da safiyar yau Laraba, 3 ga watan Satumba, 2025 a gidansa da ke Victoria Garden City (VGC) a jihar Lagos.
An haifi marigayi Akingboye a ranar 2 ga Afrilu, 1964. Shi ɗan kasuwa ne wanda ya samu nasarar a harkokin kasuwanci, kuma mutum ne mai taimako kuma jagoran al’umma.
Har zuwa lokacin rasuwarsa, shi ne Shugaba a kamfanin Benshore Maritime da Clog Oil Systems, sannan kuma shugaban WeAfrica Group.
Bugu da ƙari, Bamidele Akingboye yana rike da sarautar gargajiya ta Olowomeye I na Ikaleland, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.
Marigayin ya bar mata, ‘ya ’ya, jikoki da ‘yan uwa. Iyalansa sun bayyana cewa za su sanar da shirye-shiryen jana’izarsa a nan gaba.
Ondo: Shugaban SDP ya mika sakon ta'aziyya
Shugaban jam’iyyar SDP a jihar Ondo, Ebenezer Akinbuli, ya yi alhini da jimamin rasuwar Akingboye.
Mista Akinbulo ya bayyana marigayi Bamidele Akingboye a matsayin shugaba na gari wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima.

Source: Facebook
“Lokacin yakin neman zaben da ya yi kafin zaben 2024 a Ondo, Akingboye ya bayyana manufarsa ta ganin an gina kyakkyawar makoma ga Jihar Ondo, ta hanyar nagartaccen shugabanci, adalci ga jama’a, da ci gaba mai ɗorewa.
"Salon jagorancinsa da kwazo sun kasance abin koyi ga mutane da dama, kuma ba za a manta irin gudummuwar da ya bayar wajen ci gaban jiharmu ba."
- Ebenezer Akinbuli.
Ya yi addu’a ga mamacin, inda ya roki Allah Ya masa rahama tare da mika ta’aziyya ga iyalai, abokai da magoya bayansa.
Tsohon Sufetan 'Yan Sanda ya rasu a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban rundunar yan sandan Najeriya, Solomon Ehigiator Arase ya rasu a babban birnin tarayya Abuja.
Solomon Ehigiator Arase, wanda shi ne Sufeto Janar na 18 a Najeriya ya rasu ya na da shekaru 69 a duniya kamar yada rundunar yan sanda ta tabbatar.
Kayode Egbetokun ya kai ziyara ta’aziyya ga iyalan marigayin a Abuja, inda ya mika sakon jaje a madadin rundunar da kuma bayyana gudummuwarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

