'Abin da Ya Hana Ni Daƙile Matsalar Tsaro cikin Mako 2 a Zamfara,' Gwamna Dauda Ya Koka

'Abin da Ya Hana Ni Daƙile Matsalar Tsaro cikin Mako 2 a Zamfara,' Gwamna Dauda Ya Koka

  • Mai girma Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi magana kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi jihar
  • Gwamna Dauda ya jero wasu dalilai da suka hana shi samun damar kawo karshen rashin tsaro har zuwa yau
  • Ya bayyana cewa ya san inda manyan ’yan ta’adda suke, amma matsalar ita ce rundunonin tsaro na karɓar umarni daga Abuja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi tone-tone game da matsalolin rashin tsaro a jiharsa.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana dalillai masu yawa da suke kawo cikas da zai iya kawo karshen ta'addanci a Zamfara.

Gwamna Dauda ya yi alfahari kan matsalar tsaro a Zamfara
Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Zamfara: Gwamna Dauda ya magantu kan tsaro

Rahoton Aminiya ya ruwaito gwamna Dauda na cewa idan da yana da iko da jami’an tsaro, da zai iya warware matsalar tsaro cikin mako biyu kacal.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci

Gwamnan ya ce ya san inda ’yan bindiga ke buya a jihar, yana mai jaddada cewa wannan babbar matsala ce da ke damun jama’a.

Ya ce babban cikas a yaki da su shi ne rashin iko da jami’an tsaro, domin rundunonin suna karɓar umarni daga Abuja, ba wurinsa ba.

A cewarsa:

“Wallahi na san duk inda waya manyan ’yan bindiga suke da maboyarsu a Zamfara, kuma duk inda suka fita na sani.
“Ko a yanzu a wayata zan iya nuna muku inda wadannan ’yan ta’addan suke a yau, sai dai babu abin da za mu iya yi musu.
“Ko a yau wallahi idan ina da iko da jami’an tsaro, ina tabbatar maka za mu kawo karshen ’yan bindiga cikin wata biyu.”
Gwamna Dauda ya fadi kalubalen matsalar tsaro a Arewa
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare yayin taro a Gusau. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Irin halin da gwamna ke shiga kan ta'addanci

Dauda Lawal ya ce yakan zubar da hawaye duba da halin da al'ummarsa ke ciki game da hare-hare, sai dai ba shi da ikon bayar da umarnin daukar mataki.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin baiwa jihar Legas fifiko wajen ayyukan raya kasa

Gwamna Dauda Lawal ya ba da misali da wani hari a Shinkafi, inda jami’an tsaro suka ki zuwa saboda sun ce ba su samu umarni daga Abuja ba.

Ya ce duk da haka gwamnatin jihar na ci gaba da tallafawa jami’an tsaro da kayan aiki da kudi, sannan bayanan nan a fili suke.

A kwanakin baya, gwamnati ta ba da kyautar motocin sintiri 150 ga jami’an tsaro, ciki har da sojoji, ’yan sanda da DSS.

Gwamnan ya kuma ce ya ɗauko mafarauta sama da 2,000 daga jihohin Borno da Yobe don su taimaka wajen yaki da ’yan bindiga a Zamfara.

Dauda Lawal ya roki Allah kan ta'addanci

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummomin da ‘yan bindiga suka kai hari a Kauran Namoda inda ya yi Allah wadai da kisan.

Dauda Lawal ya ce Allah SWT zai tona asiri ya kuma wulakanta masu daukar nauyin ‘yan bindiga, yana kira ga jama’a da su dage da addu’a.

Ya yi alkawarin inganta tsaro da samar da ababen more rayuwa kamar hanyoyi, wutar lantarki, ruwa da harkokin sadarwa a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.