'Yan Bindiga Sun Cinnawa Gidaje 30 Wuta a Filato, Mutum 300 Sun Shiga Garari
- Fiye da mutane 300 ne suka rasa matsuguninsu bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Qua’an-Pan a Plateau
- Akalla gidaje 30 ne suka cinye da wuta kurmus a cikin hare-haren da suka shafi kauyuka 10 a yankin Doemak na jihar
- Shugaban karamar hukumar, Christopher Manship, ya yi kira ga shugabannin gargajiya da addini su hada kai domin kawo karshen matsalar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato – Tashin hankali ya sake barkewa a karamar hukumar Qua’an-Pan ta jihar Plateau inda mutane sama da 300 suka rasa matsugunansu.
Akalla gidaje 30 ne suka kone kurmus sakamakon hare-haren da wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka kai.

Source: Original
Leadership ta wallafa cewa an kai hare haren ne a makon da ya gabata, a dai-dai lokacin da manoma ke shirin fara girbar amfanin gona daga gonakinsu.

Kara karanta wannan
DSS ta gurfanar da manyan wadanda ake zargi da hannu a hare-haren jihohi 2 na Arewa
Matsalar da aka shiga bayan harin Filato
Harin ya kara tsananta halin da ake ciki a yankin da jama'a da dama suka dogara da noma a matsayin hanyar rayuwa.
Daraktan yada labarai na ofishin shugaban karamar hukumar, Danaan Cletus Sylvanus ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Jos.
Kauyukan Filato da aka kona gidaje
A cewar sanarwar, kauyukan da abin ya shafa sun hada da Nteng, Doop, Zhep Morop, Gyeergu, Kelaghan, Loon, Kwakii, da Gorom, duk a cikin gundumar Doemak.
Rahotannin sun nuna cewa 'yan bindigar sun kona gonaki da dakunan ajiye amfanin gona, abin da ya kara jefa manoma cikin rudani da rashin tabbas game da makomarsu.
Hari ya zo ne a lokacin da ake kuka da lamarin tsaro a wasu sassan jihar Filato, lamarin da ke ci gaba da janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

Source: Twitter
Matakan da gwamnati ta dauka da kiran hadin-kai
The Cable ta rahoto cewa shugaban karamar hukumar Qua’an-Pan, Christopher Manship, ya nuna takaici kan hare-haren da aka kai.
Ya yi kira ga shugabannin gargajiya, shugabannin addini, da kungiyoyi da su hada kai da gwamnati wajen samar da mafita mai dorewa.
A yayin wani taron tsaro da aka gudanar a Doemak, Manship ya bayyana cewa an tura jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa domin tabbatar da tsaro da dawo da zaman lafiya.
Ya kara da cewa gwamnatin karamar hukumar na aiki tukuru don dawo da zaman lafiya da tabbatar da komawar mutanen da suka rasa matsuguninsu cikin koshin lafiya.
Maganar shugabannin gargajiya
Shugaban rikon kwarya na majalisar gargajiya ta Qua’an-Pan, Safiyanu Allahnanan, ya jaddada cewa shugabannin suna da muhimmiyar rawa wajen dawo da zaman lafiya a yankunan.
Ya ce wajibi ne a hada karfi da karfe tsakanin shugabannin gargajiya, shugabannin addini, jami’an tsaro da al’umma domin shawo kan wannan matsalar.
An kai hari masallaci a jihar Kwara
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari wani masallaci a jihar Kwara.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan su kai harin ne yayin da mutane ke tsaka da sallar Isha da daddare.
A yayin da suka dura masallacin, sun yi kokarin tafiya da wani mutum amma ya yi gardama, hakan ya jawo suka harbe shi har lahira.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

