"Akwai Sauran Gurabe": Tinubu Ya Kwantar da Hankalin 'Yan Kungiyar Buhari

"Akwai Sauran Gurabe": Tinubu Ya Kwantar da Hankalin 'Yan Kungiyar Buhari

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya samu ganawa da mambobin kungiyar Buhari wadamda suka kai masa ziyara a fadar Aso Rock Villa
  • Mai girma Bola Tinubu ya sanar da su irin kalubalen da yake fuskanta wajen tattaro sunayen mutanen da yake ya nada mukamai
  • Bayan watanni 27 da shiga ofis, ya nuna cewa har yanzu guraben da za a iya ba su domin su dangwali romon shiga cikin gwamnati

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce tattara sunayen wadanda za a nada matsayin jakadu aiki ne mai matukar wahala.

Shugaba Tinubu dai har yanzu bai fitar da sunayen jakadun da za su wakilci Najeriya a kasashen waje ba, kusan shekaru biyu bayan ya hau mulki.

Shugaba Tinubu ya ce ba zai iya ba kowa mukami ba
Hoton shugaban kasa Bola Tinubu tare da Umar Tanko Almakura Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a ranar Talata lokacin da mambobin Kungiyar Buhari suka kai masa ziyara a fadar shugaban kasa da ke Abuja, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya 'tabbatar' da tazarcen Tinubu, ya ce a jira 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu: Ba kowa zai samu mukami ba

Shugaban kasar ya bayyana cewa ba zai iya nada kowa mukami ba, inda ya roki a yi masa hakuri da kuma fahimtarsa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Ba zan iya nada kowa a lokaci guda ba, na gode da hakurinku. Har yanzu ina da wasu guraben mukaman jakadu da mutane da dama ke nema."
"Amma ba abu ne mai sauki ba tattaro wadannan sunayen."

- Shugana Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta fi ba da fifiko ga daidaita tattalin arzikin kasar nan.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ta samu damar karfafa darajar Naira da kara kudin shiga ba tare da yin rance ba.

"Lokacin da na hau mulki, dala daya ta kai N1,900. Yanzu ta sauka zuwa N1,450. Farashin yana daidaituwa, kuma ba sai ka san gwamnan CBN ba kafin ka iya yin cinikin musayar kudi."
"Abin da kake bukata kawai shi ne fitarwa da shigo da kaya, sannan ka samar da ayyukan yi ga mutane."

Kara karanta wannan

Shugaban yakin zaben Tinubu ya juya baya, ya yi wa APC barazanar faduwa a 2027

- Shugaba Bola Tinubu

A baya an ji yadda gwamnatin tarayya ta nemi cin bashin kudi. Baya ga haka Legit Hausa ta lura da yadda karya Naira ya jawo ta Dala ta kai N1900 a 2023.

Tinubu ya damu da bangaren noma

Shugaba Tinubu ya kara da cewa gwamnatinsa na baiwa bangaren aikin gona muhimmanci ta hanyar amfani da kayan aiki na zamani domin karfafa samar da abinci.

Shugaba Tinubu ya ba da fifiko kan bangaren noma
Hoton shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook
"Abin da zan iya alkawarta muku shi ne daga inda muka fara zuwa inda muke nufa. Mun shiga tafarkin farfadowar Najeriya… muna kan hanya."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaban kasa ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da dorawa kan ayyukan alherin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.

Kwankwaso ya soki El-Rufai kan taba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban kusa a jam'iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi kalamai masu kaushi kan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

"Mayunwata ne": Hadimin Tinubu ya caccaki El Rufai da masu son kifar da shugaban kasa

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana cewa babu wani sharrin tsohon gwamnan da zai yi tasiri a kan mai girma Bola Tinubu.

Jigon na APC ya nuna cewa El-Rufai yana sukar gwamatin Tinubu ne don cimma manufar tunzura 'yan Arewa a kan shugaban kasan na Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng