Biyan 'Yan Bindiga Kudi: Baba Ahmed Ya Yi Wa El Rufai Raddi Mai Zafi
- Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na LP a zaben 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi martani ga Nasir El-Rufai
- Yusuf Datti Baba-Ahmed ya tanka ne bayan tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da daurewa 'yan bindiga gindi
- Ya yi zargin cewa akwai hannun jam'iyyar APC mai mulki kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya soki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya soki El-Rufai ne kan ikirarin da ya yi cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana biyan ‘yan bindiga kudi.

Source: UGC
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Politics Today' na Channels tv a ranar Talata, 2 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya soki Nasir El-Rufai
Fitaccen 'dan adawar ya bayyana cewa tsohon gwamnan na Kaduna shi ma ba zai iya wanke kansa daga laifin ba.
Ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da yin amfani da rashin tsaro a matsayin makamin siyasa.
"El-Rufai ba zai iya wanke kansa ba domin shi ma cikin lamarin yake."
"Abin da na fi damuwa da maganar Nasiru shi ne cewa shi cikakken dan APC ne tun daga 2013. Kamar yadda ya fada maku, shi ne daya daga cikin masu tsara duk wannan."
"Amma a yanzu sai ya zo yana son wanke kansa. A’a. Nasiru yana cikin abin da ke faruwa gaba daya. Mun sha wuya, mu ne wadanda muka azabtu saboda mulkin Nasiru a Zaria.”
- Yusuf Datti Baba-Ahmed
Wane zargi ya yi kan gwamnatin APC?
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi zargin cewa APC ke kitsa rashin tsaro tare da siyasantar da shi.

Kara karanta wannan
Baba Ahmed ya fadi abin da ya kamata a yi wa El Rufai kan zargin ba 'yan bindiga kudi

Source: Twitter
"Na shiga cikin radadi matuka, ku gaskata ni. Ya kamata Najeriya ta zama kasa mai girma, amma muna da mutane da suke lalata mu a kowane lokaci."
"Rashin tsaro ya kasance wani makami na APC wajen rike mulki, kuma Nasiru shi ne ya fadi hakan."
"Ina ganin yana da gaskiya, gwamnati tana biyan su. Rashin tsaro ya kasance hanyar APC ta ci gaba da zama a kan mulki. Wannan shi ne ra’ayina na gaskiya, wanda irin kalaman Nasiru suka kara tabbatarwa."
- Yusuf Datti Baba-Ahmed
An bukaci a binciki Nasir El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar na mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 karkashin inuwar jam'iyyar LP, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya bukaci hukumomi su binciki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bukaci a binciki El-Rufai ne kan zargin da ya yi na cewa gwamnatin Bola Tinubu, ta na ba da kudade ga 'yan bindiga.
Ya bayyana cewa zargin da El-Rufai ya yi ba karami ba ne, don haka bai kamata a kyale shi ya tafi haka nan a banza ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
