Gwamnatin Tinubu Ta Kawo Shirin NASAP domin Koya wa Matasa 100,000 Ayyuka
- Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin horar da matasa 100,000 ayyuka tare da ba su takardar shaidar kwarewa a dukkan jihohin Najeriya
- An sanar da wannan shiri ne a Abuja bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ma’aikatar gidaje da kamfanin Polaris Capital
- Shirin zai gudana ne a tsawon shekaru uku tare da samar da dandalin yanar gizo da zai hada kwararru da masu neman ayyuka kai tsaye daga ko ina
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Gwamnatin tarayya ta ce ta fara shirin horar da matasa 100,000 aikin gine-gine a fadin Najeriya domin cike gibi da ake da shi a bangaren gidaje da gini.
An kaddamar da shirin ne ta hannun ma’aikatar gidaje da ci gaban birane a hadin gwiwa da kamfanin Polaris Capital.

Kara karanta wannan
Likitoci sun yi tsayin daka kan tafiya yajin aiki, sun fadi yadda gwamnati ke muzguna masu

Source: Twitter
Ma'aikatar gidaje ta wallafa a X cewa ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a ranar Talata, 2 ga Satumba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan horo da takardar shaidar aiki, za a hada kwararrun da aka horas da su da ayyuka kai tsaye ta hanyar amfani da wata sabuwar manhaja ta yanar gizo.
Abubuwan da shirin NASAP ya kunsa
Sanarwar ma’aikatar gidaje ta bayyana cewa wannan mataki na daya daga cikin shirin kasa baki daya da aka yi domin rage karancin kwararru a bangaren gine-gine.
Shirin zai samu kudi daga kasafin gwamnati, 'yan kasuwa masu zaman kansu da kuma tallafi daga kungiyoyi.
Hakazalika, shirin ya kunshi sana’o’i daban-daban kamar gini, gyaran famfo, fannin lantarki, fenti, walda, kafinta, zane, gyaran na'urar sanyaya yanayi (AC) da sauran muhimman fannoni.
Maganar ma’aikatar gidaje kan shirin
Babban sakataren ma’aikatar gidaje, Dr Shuaib Belgore, wanda ya rattaba hannu kan yarjejeniyar, ya ce shirin zai kawo sababbin tsare-tsare wajen inganta kwararrun ma’aikata.
Ya kara da cewa za a baiwa matasa, mata da masu bukata ta musamman damar shiga, domin karfafa damammakin aikin yi a cikin kasa.
A cewarsa, shirin zai taimaka wajen bunkasa fasaha, samar da ci gaba mai dorewa, da kuma magance matsalar rashin kwararru a bangaren gine-gine.

Source: Twitter
Shirin NASAP zai rage rashin aikin yi
Rahoton Channels TV ya nuna cewa shugaban kamfanin Polaris Capital, Kelvin Vihishima, ya ce hadin gwiwar muhimmin mataki ne wajen rage rashin aikin yi a Najeriya.
Ya ce samun takardar shaidar aiki zai rage ayyukan wadanda ba kwararru ba, tare da tabbatar da cewa akwai isassun kwararru a bangaren gine-gine a fadin kasa.
Vihishima ya kara da cewa shirin zai taimaka wajen inganta gidaje da kuma kawo tsari mai dorewa a fannin gine-gine.
Shirin zai gudana a matakai uku: Gwaji a 2025 da zai kunshi horar da ma’aikata 3,000 a jihohi uku, fadada shi zuwa jihohi gaba daya a 2026, sannan a kafa cibiyoyin kwararru a 2027.
Legit ta tattauna da Salamatu
Wata matashiya daga jihar Filato mai suna Salamatu Muhammad Kabir ta bukaci gwamnatin tarayya ta sanya sana'o'in da za su dace da mata a cikin shirin.

Kara karanta wannan
Likitoci sun shata wa gwamnatin Tinubu layi, za su dauki mataki a cikin kwanaki 10
A cewar ta:
"Ba a bar mata a baya ba wajen dogaro da kai, ya kamata a ce mu ma an kawo shirin da zai tallafa mana.
"Idan sako na zai kai gare su, ina kira da su sake nazari game da mu, mata."
Kamfanin Teckopi ya horar da matasa
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin fasahar zamani na Techopi ya horar da matasa 20 a jihar Gombe.
Shugaban kamfanin, Usman Usman ya bayyanawa Legit Hausa cewa an gudanar da horon ne a jami'ar jihar Gombe.
Wacce ta jagoranci shirin, Aishatu Lamido ta ce an shirya shi ne domin ba matasan damar yin kafada-da-kafada da takwarorinsu a duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
