Sojoji Sun Yi Barin Wuta, an Kashe 'Yan Ta'adda, An Kwato Kayan Hada Bama Bamai
- Sojojin Operation Hadin Kai sun hallaka ’yan ta’adda fiye da 20 a wani samame da suka kai tsakanin 23 zuwa 30 ga watan Agusta 2025
- An kama masu taimaka wa ’yan ta’adda tare da gano makamai, bama-bamai da buhunan takin zamani a wajen wadannan 'yan ta'addan
- Rundunar ta ce nasarar ta kawo tsaiko ga hanyar samun kayayyakin da ’yan ta’adda ke amfani da su wajen kera bama-bamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno – Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun samu nasarar hallaka ’yan ta’adda 20 tare da cafke wasu masu taimaka musu a fadin Arewa maso Gabas cikin mako guda.
Samamen ya gudana ne tsakanin 23 zuwa 30 ga watan Agusta 2025 a karkashin shirin Operation Hadin Kai, wanda ke yaki da ta’addanci a yankin.

Source: Facebook
Rahoton da jaridar Vanguard ta fitar ya nuna cewa hare hare da aka kai zai dakile shirin 'yan ta'adda na kai farmaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar soji ta ce dakarun sun kuma kwato makamai, harsasai, bama-bamai da kayan abinci da dama da aka tanada domin taimaka wa ’yan ta’addan.
Wuraren da aka kashe 'yan ta'adda
Rahoto ya nuna cewa samamen ya gudana a wurare daban-daban na jihohin Borno da Yobe ciki har da Gujba, Gubio, Sabsawa, Whumtakum, Mandarari, Gajigana, Konduga, Banki da Loskori Kura.
A cewar majiyar, an samu hadin kai daga rundunar sojin sama da kuma kungiyoyin tsaro masu sa-kai domin taimakon hukumomi.
Wannan ya ba dakarun damar cin nasara a wurare da dama da ake zargin ’yan ta’adda suna fakewa da kuma samun kayayyaki.
Makaman da jami'an sojoji suka kwato
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa sojojin sun kwato bindigogi AK-47, bama-bamai da harsasai masu yawa.

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun toshe kofofin tsira ga 'yan ta'addan Boko Haram, an kashe miyagu
Haka kuma an gano bama-bamai da aka dana a wasu wurare, inda jami’an warware bam suka yi nasarar tarwatsa su.
Wani babban abu da aka gano shi ne buhunan takin zamani NPK guda 242 da aka tanadar domin kai wa ’yan ta’adda.
An bayyana cewa takin NPK na daga cikin muhimman sinadarai da ’yan ta’adda ke amfani da shi wajen hada bama-baman da suke tayarwa a wurare.
Tasirin nasarar sojojin a Borno da Yobe
Majiyar ta ce wannan samame ya dakile hanyoyin samun kayayyakin aiki da abinci na ’yan ta’adda, abin da zai kawo cikas ga shirinsu a nan gaba.
Ta kara da cewa hakan zai baiwa al’umma damar gudanar da harkokin kasuwanci da noma cikin walwala a yankunan da aka kakkabe ’yan ta’addan.
Babban kwamandan rundunar ya jinjinawa sojojin da suka gudanar da wannan aiki cikin kwarewa da jajircewa.

Source: Facebook
Ya kuma tabbatar musu da cewa gwamnati da rundunar sojin kasa za su ci gaba da tallafa musu domin tabbatar da dorewar nasarar da ake samu a yakin da ake yi da ta’addanci.
An kama masu garkuwa a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane da ake zargi da garkuwa da mutane.
Legit Hausa ta gano cewa wani daga cikin wadanda masu garkuwar suka taba sacewa ne ya tona musu asiri bayan ya kubuta.
Shugaban masu garkuwa da mutanen ya amsa cewa yana da hannu a sace-sacen mutane da ake a wasu sassan jihar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

