'Yan Bindiga Sun Tare Hanya, an Yi Awon Gaba da Basarake a Kogi
- An shiga juyayi da firgici bayan wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun dana tarko ga wani basaraken gargajiya a jihar Kogi
- Miyagun 'yan bindigan dai sun yi awon gaba da basaraken ne a wani wuri da ya yi kaurin suna wajen tare mutane a tafi da su zuwa cikin daji
- Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ya bayyana irin namijin kokarin da take yi don ganin an kubutar da basaraken daga hannun 'yan bindigan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kogi - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani basarake a jihar Kogi.
'Yan bindigan sun sace Hakimin Bagaji Odo a karamar hukumar Omala ta jihar Kogi, David Wada.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa 'yan bindigan sun sace basaraken ne a ranar Litinin, 1 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda 'yan bindiga suka sace basaraken
David Wada yana kan hanyarsa ne ta dawowa daga taron sarakunan gargajiya a Abejukolo, hedikwatar Omala, lokacin da lamarin ya auku.
Basaraken ya fada tarkon ‘yan bindigan ne a yankin Ojuwo Ugweche, kimanin karfe 5:00 na yamma a ranar Litinin.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun tare shi ne, sannan kuma su ka yi awon gaba da shi cikin daji, rahoton Leadership ya tabbatar.
Mazauna yankin sun ce Ojuwo Ugweche ya zama sanannen wurin garkuwa da mutane, duk da a bayan an taba tura jami’an tsaro da 'yan sa-kai domin dakile hare-hare.
Wani mazaunin yankin mai suna Maji Ahiaba ya bayyana cewa a lokacin da lamarin ya auku, babu jami'an tsaro a wurin.
"Abin bakin ciki, babu wani jami’in tsaro a ranar Litinin, wanda hakan ya ba ‘yan ta’addan damar yin abin da suka ga dama."
- Maji Ahiaba
Yayin da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Onun na Ife kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Omala, Mai Martaba Boniface Musa, ya roki a gaggauta ceto Hakimin.

Source: Original
'Yan sanda dauki matakin ceto basaraken
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP Williams Aya, ya bayyana cewa an tura jami’an tsaro da 'yan sa-kai domin su bazama cikin dazuka wajen nemo wanda aka sace.
A halin da ake ciki, tsoro ya mamaye iyalan hakimin da al’ummarsa domin har yanzu masu garkuwar ba su tuntubi kowa ba tun bayan faruwar lamarin.
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- Rashin tsaro: El Rufai ya fallasa abin da gwamnatin Tinubu ke yi wa 'yan bindiga
- An gudu ba a tsira ba': Sarki ya faɗi yadda mutane 13 suka mutu a kogi a tsarewa yan bindiga
- 'Yan bindiga sun sha wuta hannun sojojin sama, sun sako mutanen da suka sace a Zamfara
Miyagun 'yan bindiga sun kai hari a Kwara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wani masallaci da ke jihar Kwara.

Kara karanta wannan
Karshen alewa: Ƴan sandan Najeriya sun cafke Yusuf, fitaccen mai garkuwa da mutane
'Yan bindigan sun hallaka wani mutum daya har lahira yayin da suka yi kokarin yin awon gaba da shi a cikin masallacin.
'Yan bindigan dai sun dira cikin masallacin ne lokacin da al'ummar Musulmi su ke tsaka da gudanar da sallar Isha'i.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

