Shugaba Tinubu Ya Damu da Matsalar Rashin Tsaro a Katsina, Ya Dauki Mataki
- Wata tawaga daga jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda, ta gana da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- A yayin ganawar, Shugaba Bola Tinubu ya nuna takaici kan yadda 'yan bindiga suke addabar mutanen jihar
- Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa ya ba dakarun sojoji umarni lura da hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a jihar Katsina
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja -Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi magana kan matsalar rashin tsaro a jihar Katsina.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa rundunar sojoji za ta tura kayan yaki na zamani da na’urorin sa ido a jihar Katsina domin dakile yawaitar hare-haren ’yan bindiga kan fararen hula.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwa Dada Olusegun ya sanya a shafin X, wadda ke dauke da sa hannun mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga.
Bola Tinubu ya tarbi tawaga daga Katsina
Onanuga ya ruwaito shugaban kasan ya faɗi hakan ne yayin da ya karɓi tawagar fitattun ’yan jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Radda a fadar shugaban kasa.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gwamnatin tarayya za ta yi la’akari da kafa ’yan sandan jihohi.
Me Tinubu ya ce kan rashin tsaron Katsina?
“Kalubalen tsaro da muke fuskanta abin da za mu iya shawo kansa ne. Eh, muna da iyakoki masu rauni. Mun gaji wasu matsaloli da ya kamata a gyara tun da wuri. Amma kalubale ne da dole mu magance, kuma muna kokarin hakan."
“A yau na umarci dukkanin hukumomi tsaro da su tashi tsaye su duba tsare-tsaren da su ke amfani da su. Mun amince a sayo karin jirage marasa matuka."
- Shugaba Bola Tinubu
Ya kuma umurci a rika ba shi rahoton aikin tsaro na jihar Katsina kullum.
“Ina duba dukkan fannoni na tsaro; dole ne mu kirkiro da ’yan sandan jihohi. Muna kallon yiwuwar hakan. Za mu magance matsalar rashin tsaro."
"Dole ne mu kare ’ya’yanmu, jama’armu, hanyoyin samun rayuwa, wuraren ibada da wuraren nishaɗi. Ba za su tsoratar da mu ba."
- Shugaba Bola Tinubu

Source: Facebook
Tinubu ya yi wa Muhammadu Buhari addu'a
Hakazalika, Shugaba Tinubu ya yi addu'a ga marigayi Muhammadu Buhari.
“Lokacin da muka rasa ɗan’uwanmu, Shugaba Buhari, babban rashi ne ga kowa. Haka Allah Maɗaukaki ya so, amma ya bar mu a cikin yanayi mai kyau."
"Bai mika kasa da ta gaza ba, ko tsarin siyasa da aka lalata ba, amma ya bar tarihin nasara, wanda shi ne abu mafi muhimmanci."
- Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya soki nadin da ya yi a NTA
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya soke sauyin shugabancin da ya yi a gidan talabijin na kasa (NTA).
Shugaba Bola Tinubu ya umarci dawo da Salihu Abdullahi Dembos kan mukaminsa na shugaban NTA.
Sanarwar da aka fitar ta nuna cewa shugaban kasan ya soke sababbin nade-naden da ya yi, ciki har da na shugaba, daraktan labarai, daraktan kasuwanci da babban darakta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

