Baba Ahmed Ya Fadi Abin da Ya Kamata a Yi Wa El Rufai kan Zargin Biyan 'Yan Bindiga Kudi
- Maganganun da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi kan zargin gwamnati na ba 'yan bindiga kudade na ci gaba da tayar da kura
- Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana cewa maganar da El-Rufai ya yi, ba karamin al'amari ba ne da za a yi wasa
- Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasan a zaben 2023, ya bayyana cewa bai gamsu da martanin da hukumomi suka yi kan zargin na El-Rufai ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi magana kan zargin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi kan cewa gwamnatin tarayya na biyan 'yan bindiga kudade.
Dr. Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana cewa ya kamata a ɗauki zargin da Nasir El-Rufai ya yi kan cewa gwamnatin tarayya tana biyan kuɗi ga ’yan bindiga da muhimmanci.

Source: Twitter
Ɗan takarar mataimakin shugaban kasan na jam’iyyar LP a zaɓen 2023 ya yi wannan bayani ne a ranar Talata, yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufai ya yi zargi kan gwamnatin tarayya
A ranar Lahadi, El-Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya da jihar Kaduna suna biyan ’yan bindiga “kudin alawus na wata-wata” tare da aiko musu da abinci a matsayin shirin sulhu ba hanyar amfani da karfi ba.
Tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan a matsayin wani shiri na daurewa 'yan bindiga gindi.
Datti Baba-Ahmed na son a binciki El-Rufai
Sai dai, a yayin hirar, Datti Baba-Ahmed, ya bayyana cewa ya kamata hukumomi su yi wa El-Rufai tambayoyi kan kalamansa.
“Idan har ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA), zai ɗauki wannan magana da wasa, to Nuhu Ribadu bai taɓa zama ɗan sanda ba, bai cancanci zama lauya ba, bai kamata ya riƙe wannan ofis din ba."
- Datti Baba-Ahmed
Da aka tambaye shi abin da zai yi daban da shi ne mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Datti Baba-Ahmed ya ce:
"Ya kamata a sa Nasir El-Rufai ya rubuta wasu bayanai ga ’yan sanda, ga kotu.”
Ko da yake Nuhu Ribadu da gwamnatin jihar Kaduna sun musanta wannan zargi, suna kiran sa da marar tushe, Datti Baba-Ahmed ya yi watsi da martanin da suka yi.

Source: Twitter
"Wannan ba martani ba ne. Shin mutane sun fahimci girman wannan magana kuwa?"
- Datti Baba-Ahmed
El-Rufai ya zargi gwamnatin Uba Sani
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi zarge-zarge kan gwamnatin Uba Sani.
Nasir El-Rufai ya zargi gwamnatin Uba Sani da daukar nauyin 'yan daba don tarwatsa taron jam'iyyar ADC wanda ya jagoranta a Kaduna.
Tsohon gwmanan na Kaduna ya bayyana cewa suna da hujjojin da za su gabatar wadanda za su tabbatar da zargin da suke yi kan cewa akwai hannun gwamnati wajen kai harin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

