Malami: Ministan Buhari Ya Bayyana Yadda 'Yan Daba Suka Farmake Shi, Ya Nuna Yatsa ga APC
- Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami SAN, ya bayyana yadda ya fuskanci hari daga wasu da ya kira 'yan daban siyasa
- Abubakar Malami ya nuna cewa bayan ya dawo daga wata tafiya ne 'yan daban da ya kira na APC ne suka dira kan tawagarsa
- Tsohon ministan tarayyar ya bayyana cewa lamarin a matsayin abin takaici wanda ya jawo mutane da dama suka samu rauni
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami, ya yi magana kan harin da wasu 'yan daba suka kai masa a jihar Kebbi.
Abubakar Malami SAN ya bayyana yadda harin ya kasance daga tawagar 'yan daban wadda ya alakanta da jam'iyyar APC.

Source: Facebook
Abubakar Malami ya bayyana yadda lamarin ya auku ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Ga masu burin arziki: Dangote ya fadi yadda ya tara dukiya ba tare da cin gado ba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubakar Malami ya yi jawabi kan harin 'yan daba
Tsohon ministan na shari'a a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari ya ce yana dawowa ne daga fadar sarki, lokacin da kwatsam 'yan daba suka farmaki tawagar motocinsa.
A cewarsa, yana dawowa ne daga fadar Sarkin Gwandu da kuma ta’aziyya ga iyalan marigayi Imam Tukur Kola a Birnin Kebbi lokacin da aka kai wa tawagarsa hari.
Abubakar Malami ya ce 'yan daban sun kai masa harin ne a kusa da gidansa, kuma sun fito ne daga hedkwatar jam'iyyar APC wanda ke kusa da gidansa.
"An jefa mana duwatsu da mugayen makamai, an lalata motoci, mutane da dama sun samu raunuka, ciki har da karyewa"
“Abin da ya fi tayar da hankali shi ne wannan ba wani hari na bazata ba ne kawai. Shaida ta nuna wannan harin akwai siyasa a ciki."
"Manyan mutane masu karfi suka ɗauki nauyinsa, waɗanda suka yi watsi da mulki suka maida hankali kan siyasar a mutu ko a yi rai."
- Abubakar Malami
Malami ya zargi APC da hannu a harin
Ya kara da cewa akwai shaidu da ke nuna kasancewar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da kuma ’yan uwa na kusa da gwamna a wurin, lokacin da ake aiwatar da harin.

Source: Facebook
"Haka nan kasancewar jami’an tsaro ba su kawo wani taimako ba, domin ’yan daban sun koma cikin hedikwatar jam’iyya domin neman mafaka, kuma babu wanda aka kama daga bisani. An yi shiru da gangan.”
“Ya kamata gwamnatin jihar Kebbi kada ta ji tsoron Malami. Su ji tsoron sakamakon ayyukansu da kuma fushin al’ummar da aka bari cikin tsantsar talauci, rashin tsaro da kunci."
- Abubakar Malami
'Yan daba sun tarwatsa taron ADC a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan daba sun tarwatsa taron jam'iyyar ADC karkashin jagorancin Nasir El-Rufai a Kaduna.
Wasu 'yan daba dai sun dira a wajen taron dauke da adduna, duwatsu da sanduna, inda suka farmaki mutanen da ke wajen.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi Allah wadai da harin wanda ya jawo aka raunata mutane tare da lalata motocin mahalarta taron.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
