'Ko a Jiki na': Tinubu Ya Yi Martani Mai Zafi kan Harajin Trump ga Najeriya, Ya Samo Mafita

'Ko a Jiki na': Tinubu Ya Yi Martani Mai Zafi kan Harajin Trump ga Najeriya, Ya Samo Mafita

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan harajin da Donald Trump ya kakabawa Najeriya da sauran kasashen duniya
  • Tinubu ya ce Najeriya ba ta tsoron sauye-sauyen ciniki da harajin Trump, saboda tattalin arzikin kasar ya kara karfi
  • Ya kara da cewa gwamnati na daukar matakan gyaran noma da injuna don yaki da yunwa wanda hakan zai kawo karshen talauci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi watsi da matakin shugaban Amurka, Donald Trump kan kasar.

Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kasance da kwarin gwiwa, ba ta tsoron manufofin harajin Shugaba Trump.

Tinubu ya yi martani game da harajin Trump kan Najeriya
Shugaba Donald Trump da Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Donald J Trump, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Getty Images

Ya bayyana haka ne lokacin da tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Tanko Almakura da tawagarsa suka kai masa ziyarar goyon baya a Abuja, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Kura kuren da ke fitowa daga Aso Rock sun sa an taso Tinubu da hadimansa a gaba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Trump ya kakaba haraji kan kasashe

A wa’adin Trump na biyu, ya gabatar da sauye-sauyen ciniki da harajin kashi 10 bisa 100 a kan shigo da kaya daga kasashen waje.

A ranar 2 ga Afrilu 2025, Trump ya sanar da karin haraji bisa tsarin “America First,” inda ya kafa harajin kari daga kashi 11 zuwa 50.

Najeriya da sauran kasashen Afirka sun fuskanci karin haraji kashi 15 kan kayansu daga 7 ga Agusta, bayan farkon sanarwar kashi 14.

Matsalar da harajin ya jawo ga duniya

Sai dai an ware kayayyakin makamashi irin su danyen mai da iskar gas daga wannan sabon tsarin haraji da Amurka ta bullo da shi.

Rahotanni sun nuna cewa karin harajin ya jawo matsalar fitar da man fetur, gas da dizal a duniya tun farkon 2025, The Nation ta tabbatar da hakan.

Tinubu ya fadi nasararsa a fannin tattalin arziki

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa bai kamata Jonathan ya fafata da Tinubu ba a 2027'

Shugaban ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya da karuwar kudin shiga na bangaren da ba mai ba, na kare kasar daga rugujewar tattalin arziki.

Tinubu ya ce:

“Idan kudin shiga da ba na mai ba suna karuwa, to babu tsoron duk abin da Trump ke yi a can daya bangaren.”

Ya jaddada cewa Najeriya ta cimma burin samun kudaden shiga na shekarar 2025 tun watan Agusta, inda Naira ta kara daraja a kan Dala daga ₦1,900 zuwa ₦1,450.

Tinubu ya kalubalanci Trump kan haraji
Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Donald J Trump.
Source: Getty Images

Yadda Tinubu ke shirin dakile yunwa a Najeriya

Tinubu ya kuma nuna cigaba da ake samu a gyaran harkar noma, inda aka kaddamar da shirin injuna a yankuna daban-daban na kasar.

Ya ce:

“Idan muka kawar da yunwa, mun dakile talauci, tsaron abinci shi ne mabuɗin farfado da tattalin arzikin Najeriya."

Tinubu ya fadi kokarin gwamnatinsa a shekaru 2

Mun ba ku labarin cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce Najeriya tana dakile matsalolinta a karkashin shugabancinsa, inda ya bukaci goyon bayan yan Najeriya a ketare.

Tinubu ya jaddada cewa ci gaban kasa ba na gwamnati kadai ba ne, ya bukaci yan Najeriya su zama jakadun kasa a waje domin kawo ci gaba da zuba jari a jihar.

Shugaba Tinubu ya ce an inganta fannin tattalin arziki, lafiya da fasfo, tare da jawo zuba jari domin samar da ayyukan yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.