Sowore, Jafar Jafar, Hamdiyya da Wasu 'Yan Gwagwarmayar da aka Kai Kotu

Sowore, Jafar Jafar, Hamdiyya da Wasu 'Yan Gwagwarmayar da aka Kai Kotu

Jafar Jafar, Hamdiyya Sidi, Omoyele Sowore na cikin 'yan gwagwarmayar da aka taba shigar da su kara a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - 'Yan gwagwarmaya da dama a Najeriya sun sha shiga kotu wanda hakan ya yi sanadiyar kai wasu daga cikinsu gidan gyaran hali.

Matashiya 'yar jihar Sokoto, Hamdiyya Sidi na cikin wadanda aka taba kai wa kotu a kan matsalar tsaro.

Wasu daga cikin 'yan gwagwarmayar da suka yi suna a Najeriya
Wasu daga cikin 'yan gwagwarmayar da suka yi suna a Najeriya. Hoto: Omoyele Sowore|Abba Hikima|Jafar Jafar
Source: Facebook

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku jerin wasu 'yan gwagwarmayar Najeriya da aka taba shigarwa kara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Jafar Jafar ya yi shari'a da Ganduje

A 2018, Jafar Jafar mai jaridar Daily Nigerian ya wallafa bidiyon da ke nuna Abdullahi Ganduje yana saka daloli a aljihunsa, kudin da ake zargi na cin hanci daga wani ɗan kwangila ne.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tsagin Wike ya kafa sharuddan samun sulhu a jam'iyyar

A kan haka wannan zargi Ganduje ya kai ƙarar Jaafar da kamfaninsa kotu, yana mai cewa bidiyon karya ne kuma ya bata masa suna.

Jafar Jafar da ya buga shari'a da Abdullahi Ganduje
Jafar Jafar da ya buga shari'a da Abdullahi Ganduje. Hoto: Jafar Jafar
Source: Twitter

A shari'ar, babbar kotu a Kano ta ba da umarnin cewa Abdullahi Ganduje ya ba Jaafar Jaafar da kamfaninsa N800,000 a matsayin diyyar bata lokaci da kuma bata suna.

Alkalin kotun, mai shari'a S.B. Namalam, ya amince da bukatar lauyoyin Ganduje na janye karar amma ya tabbatar da cewa sai an biya kudin diyyar.

A yanzu haka, jami'in gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi barazanar shigar da Jafar Jafar kotu kan kiransa da barawo a kan zarginsa da badakalar makudan kudi.

2. Ana shari'a da Hamdiyya a Sokoto

Hamdiyya Sidi Shariff wata matashiya ce mai fafutuka daga jihar Sokoto da ta yi suna saboda suka ga yadda gwamnatin jiharta ke tafiyar da lamuran tsaro.

A shekarar 2024, an kama ta bayan ta wallafa wani bidiyo a TikTok da ya fito da zargin shiru da gwamnatin ke yi game da hare-haren ’yan bindiga a Sabon Birnin Daji.

An gurfanar da ita a kotu bisa tuhume-tuhumen yin amfani da kalmomin ɓatanci da kuma tayar da fitina.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda sun kama bindigogi, masu garkuwa, barayi da sauran miyagu a Kano

Hamdiyya Sidi a bakin kotun da ake mata shari'a a Sokoto
Hamdiyya Sidi a bakin kotun da ake mata shari'a a Sokoto. Hoto: Abba Hikima
Source: Facebook

Ƙungiyar kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International da wasu ƙungiyoyi sun soki kama ta da kiran lamarin a matsayin kokarin toshe ’yancin faɗin albarkacin baki.

Lauyanta, Abba Hikima ya nemi kariyar ’yan sanda masu dauke da makamai a duk lokacin zaman kotu saboda barazanar da suke fuskanta.

3. Sowore ya sha shari'a da gwamnati

'Dan jarida mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama kuma wanda ya kafa Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ya sha fuskantar shari’o’i a kotunan Najeriya.

Sowore ya yi fama da zuwa kotu ne saboda tsananin sukar da yake yi wa cin hanci da rashawa da kuma kira da yake yi na kawo sauyi.

A Agustan 2025, lauyan Sowore ya bayyana cewa an tuhume shi da ɓata suna bayan wata gayyatar da ’yan sanda suka yi masa.

Sowore da wasu mutane a filin zanga zanga
Sowore bayan 'yan sanda sun sake shi a Abuja a 2025. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

A yanzu haka, Sowore na zuwa kotu domin fuskantar shari'ar da rundunar 'yan sandan Najeriya ta shigar da shi.

Kara karanta wannan

Kura kuren da ke fitowa daga Aso Rock sun sa an taso Tinubu da hadimansa a gaba

4. Kotu ta daure IG Wala a Abuja

A 2019 aka yankewa Ibrahim Garba Wala da aka fi sani da IG Wala hukuncin zama gidan yari na shekara bakwai ta hannun Mai Shari’a Yusuf Halilu na Babbar Kotun Abuja.

Premium Times ta rahoto cewa an same shi da laifin yin ƙarya kan zargin shugaban hukumar aikin hajji, Abdullahi Mukhtar da cin hanci tare da jagorantar zanga-zanga a kansa.

IG Wala a lokacin da ya ziyarci jihar Kebbi bayan fita a kurkuku.
IG Wala a lokacin da ya ziyarci jihar Kebbi bayan fita a kurkuku. Hoto: IG Wala
Source: Twitter

Mai shari’a Halilu ya same shi da laifi a cikin tuhuma uku daga cikin huɗu da Sufeton ƴan sanda na ƙasa tare da Babban Lauyan Ƙasa suka shigar da shi.

Sai dai daga baya, dan gwagwarmayar ya samu fita daga gidan gyaran hali saboda afuwar da marigayi shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa wasu fursunoni.

5. Agba Jalingo ya fita daga kurkuku

Mawallafin shafin CrossRiverWatch, Agba Jalingo, ya samu ’yanci bayan mako guda a gidan gyaran hali na Kuje, Babban Birnin Tarayya Abuja.

Vanguard ta wallafa cewa an saki Jalingo ne bayan da aka tsare shi a kurkuku bisa umarnin mai shari’a Zainab Abubakar ta babbar kotun tarayya kan zargin bata suna.

Kara karanta wannan

An kama tarin makamai ana kokarin shiga da su Katsina daga Jigawa

Agba Jalingo yayin da ake gurfanar da shi a kotu
Agba Jalingo yayin da ake gurfanar da shi a kotu. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

An gurfanar da shi ne kan tuhumar wallafa labaran ƙarya da ake zargin an yi domin bata wa wata mata mai alaka da gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade suna.

An rahoto tsohon gwamnan yana zarginsa da neman kifar da gwamnatin Muhammadu Buhari.

'Dan Bello ya shiga zanga zanga a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa an yi zanga zangar 'yan sanda a birnin tarayya Abuja da wasu jihohin Najeriya.

'Dan gwagwarmaya, Dan Bello da wasu masu fafutuka a Najeriya da suka hada da Omoyele Sowore sun jagoranci zanga-zangar.

Legit ta rahoto cewa an yi zanga zangar ne domin hakkokin tsofaffin 'yan sanda da ba su fitowa yadda ya kamata bayan kammala aiki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng