Agba Jalingo ya yi yunkurin hambarar da gwamnatin Buhari ne - Gwamna Ayade

Agba Jalingo ya yi yunkurin hambarar da gwamnatin Buhari ne - Gwamna Ayade

Gwamnan Cross Rivers Ben Ayade ya ce an cigaba da tsare dan jarida Agba Jalingo ne saboda rawar da ya taka yayin zanga-zangar juyin juya hali na 'Revolution Now'.

Daily Trust ta ruwaito cewa Ayade ya yi wannan jawabin ne a jiya a gidan gwamnati a Abuja yayin zantawa da manema labarai bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari.

Ana tuhumar Jalingo, mawallafin Cross River Watch, da laifin cin amanar kasa. An kama shi ne tun a watan Augustan 2019 kan wata rahoto da ya wallafa na cewa Ayade ya karkatar da Naira miliyan 500 na jihar.

Ayade ya ce yanzu shi ba dan jarida bane, ya ce shi ne shugaban jam'iyyar African Action Congress wacce mawallafin Sahara Reporters Omoyele Sowore ya kafa.

Agba Jalingo ya yi yunkurin hambarar da gwamnatin Buhari ne - Gwamna Ayade
Agba Jalingo ya yi yunkurin hambarar da gwamnatin Buhari ne - Gwamna Ayade
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota

Gwamnan ya ce, "Tunda ya fara fafutikan neman hambarar da gwamnatin Shugaba Buhari, an dena masa kallon dan jarida saboda ya zama shugaban jiha na jam'iyyar siyasa.

"A court, gwmanatin tarayya ne ke shari'a da Agba Jalingo ba gwamnatin Cross Rivers ba. Agba Jalingo da ke tsare a gidan yari na kan tura masa kudi ...

"Amma a lokacin da nayi kuskure kawai sai ka tafi dandalin sanda zumunta kayi rubutu cewa Gwamna Ayade ya dauke Naira miliyan 500 ya kai Rasha. Ka bata min suna da na iyaye na saboda kawai ban cika maka wata bukata ba duk da cewa ina yi maka a baya. Idan kai ne ke halin da na ke ciki ya za kayi. Ni abinda nayi kawai na janye hannu na daga batun ne.

"Ana tuhumarsa da laifin cin amanar kasa ne a kotu. Gwamnatin jihar ba ta da ikon yi wa mutum shari'a kan zargin cin amanar lasa. Ba ni bane."

Ya ce Buhari zai ziyarci jiharsa domin kaddamar da wata sabuwar shiri mai suna G-money na inganta rayuwar mutane da zai samar da ayyuka 2,000 ga mata da yara da hanyar noma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel