"Na Yi Nadama": Tsohon Hadimin El Rufai Ya Kwance Masa Zani a Kasuwa

"Na Yi Nadama": Tsohon Hadimin El Rufai Ya Kwance Masa Zani a Kasuwa

  • Daya daga cikin mutanen da suka yi aiki da Nasir El-Rufai a Kaduna, ya fito ya caccaki salon mulkinsa da yake ofis
  • Ben Kure ya jefo wasu zarge-zarge kan yadda Nasir El-Rufai ya gudanar da mulkinsa a matsayin gwamnan Kaduna
  • Tsohon hadimin na El-Rufai ya bayyana cewa sun dade suna fatan ganin an samu canji mai kyau a Kaduna bayan 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Tsohon mai ba da shawara kan harkoki siyasa ga Nasir El-Rufai, Ben Kure, yace ya yi nadamar aiki tare da tsohon gwamnan na jihar Kaduna.

Ben Kure ya bayyana cewa ya yi nadamar goyon bayan da ya ba tsohon gwamnan na jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Ben Kure ya soki Nasir El-Rufai
Hotunan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon hadiminsa, Ben Kure Hoto: Nasir El-Rufai, Ben Kure
Source: Facebook

Ben Kure ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Bayan Ribadu da Uba Sani sun yi raddi, Sanata Shehu Sani ya duro kan El Rufa'i

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon hadimin El-Rufai ya juya masa baya

Ya zargi El-Rufai da jagorantar gwamnatin da ta haifar da rarrabuwar kawuna a cikin shekara takwas da ya yi yana mulki.

Ben Kure ya ce yana ɗaya daga cikin tawagar farko da ta kafa jam'iyyar APC a jihar Kaduna, wadda daga bisani ta haifar da zaman El-Rufai a matsayin gwamna.

"Ina ɗaya daga cikin mambobin kwamitin rikon da ya kafa APC a jihar Kaduna. Na jagoranci rajistar mambobi a jihar tare da Kanal Abdullahi (mai ritaya), fitaccen Sanata M.B. Saleh, da kuma tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Birnin-Gwari da Giwa, Hon. Shehu Balarabe."

- Ben Kure

A cewarsa, El-Rufai ya shiga siyasar Kaduna ba tare da wani tushen siyasa ba, sai dai ya dogara kacokan ga jajirtattun mambobin jam’iyya domin samun tikitin takarar gwamna.

"Lokacin da Malam Nasir El-Rufai ya shigo, ya shigo siyasar Kaduna ne a matsayin wanda bai da wata kafa, babu tsarin siyasa, babu komai."

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: El Rufa'i ya yi wa Ribadu da Uba Sani wankin babban bargo

"Mu ne sojojin yakin da suka tabbatar ya samu tikitin takara ya kuma zama gwamna. Ni ne shugaban kwamitin kamfen dinsa a 2015 da kuma a 2019."

- Ben Kure

Sai dai, ya ce babban abin da yake yi wa nadama a harkar siyasa shi ne goyon bayan El-Rufai, inda ya zarge shi da yin siyasar rarrabuwar kai.

"A rayuwata, ban taɓa yin nadama kan wani abu ba kamar yadda na yi nadama kan bi ko haɗa kai don goyon bayan Malam Nasir Ahmed El-Rufai."
"Babban abin takaici shi ne, an gabatar mana da shi a matsayin ɗan kishin kasa, amma abin da muka gani daga Malam Nasir El-Rufai a cikin shekara takwas na shugabancinsa a matsayin gwamnan jihar Kaduna ba komai ba ne illa siyasar warewa, siyasar nuna bambanci da kuma siyasar rarraba kawuna"

- Ben Kure

Meyaaa Ben Kure ya ki yin murabus

Da aka tambaye shi ko ya lura da waɗannan dabi’u a lokacin da yake aiki tare da tsohon gwamnan, Ben Kure ya ce biyayyarsa ga jam’iyya ta sa ya ci gaba da kasancewa tare da shi duk da korafe-korafensa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna ta gagara hakura, ta aika da kashedi mai zafi ga El Rufai

Ben Kure ya caccaki El-Rufai
Hoton tsohon mai ba Nasir El-Rufai shawara kan harkokin siyasa, Ben Kure Hoto: Ben Kure
Source: Facebook
"Tun a duk lokacin mulkinsa mun lura da hakan, amma mun danne shi ne domin jam’iyya ta ci gaba."
"Mun yi imani cewa da yardar Allah, a nan gaba za mu samu wani shugaba da zai gyara munanan abubuwan da Malam Nasir El-Rufai ya bari ga mutanen jihar Kaduna.”

- Ben Kure

A lokacin mulkin El-Rufai Legit Hausa ta fahimci Ben Kure ya rike mukamai da suka hada da hadimi zuwa shugaban karamar hukuma a Kaduna.

Gwamnatin Kaduna ta gargadi El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna, ta yi wa Nasir El-Rufai martani mai zafi.

Gwamnatin ta ja kunnen tsohon gwamnan na jihar Kaduna kan yunkurin da ta ce yake yi na kawo hargitsi.

Ta bayyana cewa ba za ta lanunci hakan ba, kuma tuni ta ankarar da jami'an tsaro don su yi abin da ya dace.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng