'Yan Bindiga Sun kai Hari ana Sallar Ishai, Sun Kashe Rai a Kokarin Satar Mutane

'Yan Bindiga Sun kai Hari ana Sallar Ishai, Sun Kashe Rai a Kokarin Satar Mutane

  • An kashe wani mutum mai shekara 45 mai suna Alhaji Dahiru a wani yunkurin sace shi a cikin masallaci a Patigi, jihar Kwara
  • Wadanda suka kai harin sun yi ƙoƙarin tafiya da shi amma ya yi musu rashin biyayya, hakan ya sa suka harbe shi har lahira
  • Lamarin ya faru ne yayin sallar Isha’i, inda al’umma suka gano harsashi biyu na bindiga kirar AK-47 a wajen da abin ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara – Wani mummunan hari ya girgiza jama'a a jihar Kwara bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe wani mutum mai suna Alhaji Dahiru.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe shi ne a lokacin da ake ƙoƙarin yin garkuwa da shi a cikin masallaci.

Taswirar jihar Kwara da aka kai hari a masallaci
Taswirar jihar Kwara da aka kai hari a masallaci. Hoto: Legit
Source: Original

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka kai harin ne a cikin wani sako da mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Babbar mota ta murkushe Musulmi yana sauri zuwa masallacin Juma'a, an yi rikici

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka kai hari a masallacin?

Lamarin ya auku ne a ranar 30 ga watan Agusta, da misalin ƙarfe 8:30 na dare, yayin da musulmi ke tsaka da gudanar da sallar Isha’i a masallacin unguwar.

Rahotanni sun bayyana cewa, Alhaji Dahiru ya yi ƙoƙarin zillewa daga hannun masu garkuwar, abin da ya fusata su har suka harbe shi nan take.

Yadda aka kai hari masallacin Kwara

Shaidun gani da ido sun ce mutum bakwai dauke da bindigogi ne suka shiga masallacin da nufin yin garkuwa da Dahiru, amma ya ƙi tafiya da su.

Sai dai a cikin fushi, ɗaya daga cikinsu ya harbe shi a gaban jama’ar da ke cikin masallacin, wanda hakan ya jefa mutane cikin tsananin firgici.

Bayan kisan, ‘yan bindigar suka tsere da sauri a kan babura, suka bar harsashi biyu na AK-47 a wajen da abin ya auku.

Martanin jama’a da iyalan marigayin

Bayan faruwar lamarin, jama’ar garin sun bayyana bacin ransu tare da nuna tsoro kan tsaron rayuka a yankin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari Kano da dare, sun sace mata bayan kashe rai

The Cable ta rahoto cewa Iyalan mamacin sun yi kira ga hukumomi da su hanzarta bada izinin gudanar da jana’izar sa bisa ga tsarin musulunci.

Sun kuma bukaci a tabbatar da tsaro a masallatai domin kauce wa irin wannan mummunan lamari a nan gaba.

Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Kwara da kalubalen tsaro a Najeriya

Jihar Kwara na daga cikin yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro, musamman bayan bayyanar ƙungiyar 'yan ta'adda da ake kira Lakurawa a Najeriya.

Faruwar irin waɗannan hare-hare, musamman a wuraren ibada na iya kara tsananta matsalar tsaro a Arewacin ƙasar.

An kama makamai a jihar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana nasarorin da ta samu a jihar Kano a watan Agusta.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an kama 'yan daba sama da 60 yayin da aka kama barayin babura da sauransu.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama masu garkuwa da mutane takwas, makamai da suka hada da bindigogi kirar gida da AK-47.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng