Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Yankin da Ya Fi More Ayyukanta na Alheri
- Gwamnatin tarayya ta fadi yankin da ya fi kowane samun kaso mai tsoka yayin da ake ta zargin ta fifita yankin Kudancin Najeriya
- Martanin ya biyo bayan rahoton da ya nuna jihar Legas kadai ta samu fiye da jimillar kuɗin da wasu jihohi 18 suka amfana da su
- Minista yada labarai, ya ce Legas ta samu ƙarin ne saboda manyan gadoji, tasoshin jiragen ruwa da filayen jirgin sama da ke jihar.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - A Najeriya, an sha sukar gwamnatin Bola Tinubu kan nuna wariya a wasu yankunan kasar tare da fifita wasu jihohi.
Sai dai gwamnatin tarayya ta fitar da wasu bayanai da ke karyata jita-jitar da ake yadawa a fadin kasar.

Source: Facebook
Ministan yaɗa labarai, Muhammad Idris, ya tabbatar da haka a wata hira da jaridar BBC Hausa wanda aka wallafa a Facebook.
Legas ta fi jihohi 18 morar ayyukan Tinubu
Sai dai wannan ikirarin gwamnatin tarayya zai iya ba da mabambantan alkaluma idan aka sako jihar Legas a ciki.
Martanin ya zo ne bayan rahoton da ya ce kuɗin ayyukan jihar Legas kadai sun fi na wasu jihohi 18 daga shiyyoyi daban-daban.
Kenan hakan ya tabbatar da cewa idan aka cire Legas shi ne Arewa maso Yamma ta fi kowane yanki samun kaso mafi yawa.
Gwamnatin tarayya ta kare ayyukan Tinubu
Idris ya ce Arewa maso Yamma ta samu Naira tiriliyan 5.9, sannan Arewa ta Tsakiya ta samu Naira tiriliyan 1.1, cewar rahoton Punch.
Gwamnatin ta bayyana cewa shiyyar Arewa maso Yamma ta samu kaso mafi tsoka wanda ya kai kusan kashi 40 kenan a kasar baki daya.
Sai dai gwamnati ta gabatar da jadawalin kuɗaɗen da aka amince da su, inda ta nuna adadin da shiyyoyi suka samu ya sha bamban da rahoton.

Kara karanta wannan
'Na shirya rungumar zaman lafiya': Bello Turji ya dauki alkawari, ya fadi sharrin da ake yi masa

Source: Twitter
Dalilin da ya sa Legas ta fi samun ayyuka
Mohammed Idris ya ce jihar Legas ta samu Naira tiriliyan 1.2, saboda akwai manyan gadoji, tasoshin jiragen ruwa da kuma batun filin jirgi.
Ya ce hakan shi ya sa ta yi fice idan aka kwatanta da wasu jihohi ko yankunan Najeriya da jawo maganganu cewa ana fifita ta fiye da sauran takwarorinta.
Ya ce:
''Sauran kuɗin kuma wasu manyan ayyuka ne da suka haɗa da yankin kudu maso yammacin ƙasar da aiki ya shafi jihar Legas."
Tinubu ya yi alkawarin yin adalci a Najeriya
Mun ba ku labarin cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce rantsuwar da ya yi a matsayin shugaban kasa ta shafi kowa a Najeriya, ba wani yanki kadai ba.
Tinubu ya jaddada cewa dukkan ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa a sassa daban-daban na kasar na nufin ci gaban kasa baki daya ba tare da nuna wariya ba.
Shugaba Tinubu ya ce babu wani dan kasa da ya fi wani daraja, kuma babu wani yanki da za a bari a baya a tafiyar mulkinsa domin tabbatar da adalci a tsakani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
