Izala za Ta Hada Tinubu, El Rufa'i da Manyan Kasa a Taron da za Ta Yi a Kaduna
- Kungiyar Jibwis ta shirya wa’azin ƙasa da za a gudanar a Kaduna a ƙarshen mako tare da gabatar da sababbin littattafai
- Shugaban kasa, shugabannin addini, sarakuna, gwamnoni na daga cikin manyan baƙi da ake sa ran za su halarci taron
- Haka kuma an shirya tattaunawa ta musamman kan illolin masu bin Kur’ani kawai ba tare da hadisin Annabi (SAW) ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna – Kungiyar Izala ta Jibwis ta shirya wa’azin ƙasa da taron gabatar da littattafan Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da aka fassara.
Za a gudanar da wannan gagarumin taro a ranar Asabar 6 ga watan Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 9:00 na safe a jihar Kaduna.

Source: Facebook
Izala ta wallafa a shafinta na Facebook cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai kasance babban baƙo a wajen taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a gabatar da littattafan Sheikh Gumi
Daga cikin muhimman abubuwan da za a gudanar akwai gabatar da littafin Where I Stand na marigayi Sheikh Abubakar Gumi wanda Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya fassara zuwa Larabci.
Haka kuma Dr Jalo ya shirya wasu littattafai irin su Al’akidatus Sahiha, Ahlari, Izziya, Risala da Ishmawi daga tsarin zube zuwa tsarin waƙe, waɗanda za a gabatar a wannan rana.
Sanata Abdul’aziz Yari zai kasance babban mai gabatar da taron, yayin da babban limamin masallacin Sultan Bello, Sheikh Muhammad Sulaiman zai yi bita kan littattafan.
An gayyaci Tinubu da El-Rufa'i zuwa taron
Ana sa ran cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron a matsayin babban bako, yayin da Gwamnan Kaduna Uba Sani zai kasance mai masaukin baki.
Hakazalika, ana sa ran tsofaffin gwamnonin Kaduna kamar Ahmed Makarfi, Ramalan Yero da Malam Nasiru El-Rufai za su kasance a wajen taron.
Iyayen taron sun haɗa da Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III, da Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli.
A madadin iyalan marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Dr Ahmad Gumi zai yi jawabi na musamman.
Za a tattauna kan 'yan kala kato
A ranar Juma’a 5 ga watan Satumba, za a gudanar da taron tattaunawa kan illar ra’ayin masu ikirarin bin Kur’ani kawai ba tare da hadisi ba, wato ’yan Kala Kato.
Wannan taron zai gudana bayan sallar la’asar a dakin taron Umaru Musa ’Yar’adua ƙarƙashin jagorancin Dr Ibrahim Disina da Dr Abubakar Abdulsalam Baban Gwale.

Source: Facebook
Sheikh Lawal Shu’aib Triump, Sheikh Abubakar Mazan Kwarai da Sheikh Musa Muhammad Dankwano za su kasance cikin jerin malamai masu jawabi.
Wa’azi da hudubobi a masallatan Juma’a
A cikin shirin, kwamitin Da’awa na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina zai rarraba malamai zuwa masallatan Juma’a domin gudanar da hudubobi da wa’azi.
Haka kuma a ranar Asabar daga ƙarfe 8:00 na dare za a gudanar da wa’azin ƙasa a masallacin Idi na Sultan Bello, inda manyan malamai daga sassa daban-daban za su yi wa’azi.
Malamai da alarammomi daga jihohi da dama za su halarci taron ciki har da Sheikh Isa Ali Pantami, Farfesa Salisu Shehu, Sheikh Habibu Yahaya Kaura da sauransu.
Za a fara ba limamai alawus a Kastina
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kastina ta kawo shiri na musamman kan malaman addinin Musulunci.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa za a fara biyan limaman masallatan Juma'a na jihar kudin wata.
Baya ga limaman, gwamnatin ta sanar da cewa za a sanya wa masu sharar masallatan Izala da Darika na jihar alawus.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


