Ran Shehi ya Baci game da Hadin kan Malaman Musulunci, Ya Fadi Shehunnan da Yake Zargi

Ran Shehi ya Baci game da Hadin kan Malaman Musulunci, Ya Fadi Shehunnan da Yake Zargi

  • Ana ta ce-ce-ku-ce kan batun hadin kan malaman addinin musulunci a Najeriya, inda malamai suka samu bambantan ra’ayoyi
  • Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya ce bai goyi bayan hadin kan akida ba, amma ya ce idan domin gyara al’umma ne, akwai amfani yin hakan
  • Malamin ya bayyana damuwa da wasu malaman da ake zargi, yana mai cewa a hada kai wajen yakar rashawa da ‘yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Ana ta surutu daga bangarori dabam-dabam game da shirin hadin kan malaman Izalah da darika a Najeriya.

Farfesa Ibrahim Makari na daga cikin wadanda suke kan gaba don ganin an samu zaman lafiya a tsakani.

Malami ya soki masu neman hadin kan malaman Izalah da darika
Sheikh Ishaq Adam Ishaq yana daga cikin masu sukar hada kan Izalah da darika. Hoto: Barr. Ishaq Adam Ishaq.
Source: Facebook

Hada kan Musulimi: Matsayar Sheikh Ishaq Adam

Malam Ishaq Adam Ishaq ya bayyana matsayarsa kan lamarin a faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Sunnah ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke bayan tono gawar malamin Musulunci a kabari aka kona ta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Ishaq ya ce ko kadan bai goyon bayan lamarin duba da bangaren da ake neman a hada kan.

Malamin ya ce idan da ta wani bangare ne domin kawo sauyi a cikin al'umma babu matsala amma ba akida ba.

“Mutum ya ce idan ba ka yarda ba ko ba ka son Shehu Tijjani wai ba ka da imani, ko idan ba ka yadda da Maulidi ba kai ba Musulmi ba ne.
“Kuma wadannan mutane su ne suke ta magana wai a hada kai, a hada kai, a taru a hada kai, babu wanda ya ce bai kamata a hada kai ba.
“Amma idan za a hada kan, a kan meye za a yi hakan, idan haka ne akwai kungiyoyi kamar su Jama'atul Nasril Islam, wadannan duk sun kasa ne.“
Farfesa Makari yana jagorantar hada kan malaman Izalah da darika
Farfesa Makari kenan da wasu malamai a taron hadin kan Musulmi. Hoto: Prof. Ibrahim Maqari|Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi.
Source: Facebook

Shawar malamin kan shirin hada kan Musulmi

Sheikh Ishaq Adam ya ce hada kai ya danganta da me ake son cimmawa musamman da ya shafi al'umma.

Kara karanta wannan

Yadda shugaba Tinubu ke yawan nadin mukamai ya warware daga baya

Ya ce amma idan har hada kai ne na akida dole ne sai an zauna an kawo hujjoji daga ayar Alkur'ani da hadisai kan bambance-bambance.

Ya kara da cewa:

“Idan za mu hada kai, muna da sabani mu daidata kan bambance-bambancen mu misali inda aka ce Salatul Fati ta fi Alkur'ani, kawo aya ko hadisi.
“Idan kuka ce za mu hada kai ne mu je wurin gwamnati ta yi maganin yan bindiga wannan madalla.
“Mu hada kai domin hana jami'an gwamnati sata wannan abu ne mai kyau, amma idan ka yi bidi'a ko kafurci dole na fada maka kuskurenka.“

Malamin ya ce kan lamarin akwai wasu malamai da yake zargi, an ce daya dan 'Interfaith' ne da ya taba cewa idan ya samu dama a gwamnati duk wanda ya cewa wandanda ba Musulmai ba arna sai an kama shi.

Sannan ya ce akwai dayan yana Abuja duk wata fitina da za a kullawa Ahlul Sunnah shi ne, ya ci gyaran Alkur'ani ya ci gyaran hadisi.

Legit Hausa ta tattauna da dalibin ilimi

Kara karanta wannan

Trump: Amurka ta sake fitar da gargadi game da rashin tsaro a Najeriya

Wani dalibin ilimi a Gombe, Muhammad Khamis ya ce tabbas maganar Shehi gaskiya ne babu haduwa a bangaren akida.

Ya ce:

"Hadin kai na ci gaban rayuwa ba matsala ba ne amma maganar akida dole kenan sai daya ya janye na shi?."

Ya ce ai ko bangarorin Izalah da ke da akida daya ma sun gaza haduwa bare sauran akidu.

Ana shirin hada kan malaman Musulunci

Kun ji cewa tawagar Malamai da kungiyoyi ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ibrahim Makari ta kai ziyara ga manyan shugabannin addini.

An jaddada cewa haɗin kan Musulmi ba yana nufin barin mazhaba ko fahimta ba ne, illa kawar da husuma da kafirta juna.

Shugabannin da aka ziyarta sun nuna goyon baya ga wannan yunƙuri na samar da murya guda ga al’ummar Musulmi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.