Bayan Gargadin NEMA, Ambaliya Ta Afka wa Dubban Mutane a Adamawa

Bayan Gargadin NEMA, Ambaliya Ta Afka wa Dubban Mutane a Adamawa

  • Ambaliyar ruwa ta afka wa wasu yankuna a Numan sakamakon bullar ruwa daga madatsar Kiri a daren 31 ga Agusta, 2025
  • Rahoto ya nuna cewa dubban mazauna kauyuka biyar sun rasa muhallansu, ruwan ya kuma lalata gonaki da gidaje
  • Hukumomin NEMA da ADSEMA sun gudanar da bincike kai tsaye tare da gabatar da bukatar tallafin abinci da matsuguni

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wani mummunan bala’i na ambaliyar ruwa ya auku a karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa, inda dubban jama’a suka rasa matsuguninsu.

Lamarin ya faru ne sakamakon fitar ruwa daga madatsar Kiri da ya jawo ruwa ya kwarara a wuraren da jama'a ke harkokinsu.

Wasu jami'an NEMA da ADSEMA suna bayar da agaji a Adamawa
Wasu jami'an NEMA da ADSEMA suna bayar da agaji a Adamawa. Hoto: NEMA Nigeria
Source: Facebook

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta wallafa yadda ambaliyar ta yi barna a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Likitoci sun shata wa gwamnatin Tinubu layi, za su dauki mataki a cikin kwanaki 10

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barnar da ambaliya ta yi a Adamawa

NEMA da ADSEMA sun gudanar da bincike kai tsaye don tantance irin barnar da aka yi yayin da shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki suka halarci wajen.

Rahoton farko ya nuna cewa ambaliyar ta yi sanadiyyar mutuwar mutum guda, yayin da aka ruwaito an lalata gidaje, gonaki da kadarori masu tarin yawa a yankin.

Wata makarata da ambaliya ta cinye a Adamawa
Wata makarata da ambaliya ta cinye a Numan na Adamawa. Hoto: NEMA Nigeria
Source: Facebook

Ambaliyar ta auku ne da misalin karfe 10:30 na dare a ranar 31 ga Agusta, lokacin da ruwa ya balle daga madatsar Kiri.

Rahoto ya nuna cewa ruwan ya yi barna a yankuna guda biyar; Imburu, Zangun, Lure, Kwakwambe da Ngabalang.

Dubban jama’a ne suka tsinci kansu a cikin halin kaka-ni-ka-yi, inda gidaje da dama suka rushe yayin da gonaki da dama suka lalace.

Halin da jama'ar Adamawa suka shiga

A lokacin da tawagar NEMA ta kai ziyara, an samu wasu daga cikin wadanda abin ya rutsa da su suna zaune a makarantar firamare ta Imburu.

Kara karanta wannan

Sokoto: Gwamna zai fara ba limamai, ladanai da masallatan Juma'a kudin wata

Wasu kuma sun kafa rugar wucin gadi a gefen hanya, yayin da wasu suka koma wurin ‘yan uwa da abokan arziki domin samun mafaka.

Al’ummar yankin sun bayyana halin matsi da suke ciki, musamman rashin abinci, ruwan sha da kayan kwanciya.

Wannan ya nuna cewa akwai bukatar samar samar da tallafi daga hukumomi da masu hannu da shuni cikin gaggawa.

Bukatar tallafin gaggawa a Adamawa

Binciken NEMA da ADSEMA ya tabbatar da cewa akwai bukatar matsuguni, abinci da kayayyakin rayuwa na yau da kullum domin rage radadin jama’ar da abin ya rutsa da su.

Shugaban tawagar, Malam Mohammed Yaji na ADSEMA, ya jaddada bukatar daukar matakan gaggawa don kare lafiyar jama’a.

Mai magana da yawun NEMA a Yola, Hafeez Bello ya ce hukumar za ta ci gaba da aiki da hukumomin jihar da sauran abokan hulda wajen samar da tallafin da ake bukata.

NEMA ta yi gargadi game da ambaliya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta yi gargadi kan yiwuwar ambaliyar ruwa.

Kara karanta wannan

Katsina: Za a rika ba limamai, masu sharar masallatan Izala da Darika kudin wata

Hukumar NEMA ta bayyana cewa akwai fargabar ambaliyar ruwa a yankuna 14 na jihohin Arewa guda tara.

Biyo bayan gargadin, NEMA ta bukaci mutanen da suke zaune a wuraren da su gaggauta daukar matakan da ya kamata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng