Sokoto: Yan Bindiga Sun Yashe Gari Tas, Sun Sace Basarake da Duka Limaman Gari

Sokoto: Yan Bindiga Sun Yashe Gari Tas, Sun Sace Basarake da Duka Limaman Gari

  • ’Yan bindiga sun kai hari a garin Rinaye, sun kashe mutum uku, suka sace hakimi da limamai tare da wasu mutane a Sokoto
  • Ƴan gudun hijira daga kauyuka fiye da goma sun rufe hanyar Shagari-Sokoto domin nuna fushinsu ga gwamnati kan rashin tsaro
  • NEMA da SEMA sun tabbatar da halin da ake ciki, suka bukaci gwamnati ta kawo ɗaukin gaggawa da tsaro don mutanen su koma gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Al'ummar jihar Sokoto sun yi zanga-zanga game da hare-haren yan bindiga a yankunansu.

’Yan bindiga sun kai mummunan hari a garin Rinaye inda suka kashe mutum uku wanda ya tayar da hankulan al'umma.

Sakkwatawa sun yi zanga-zanga kan matsalar tsaro
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto da ke Arewacin Najeria.
Source: Facebook

Rahoton Aminiya ya ce maharan sun kuma sace mai gari da dukkan limaman garin tare da wasu mutane.

Kara karanta wannan

Sokoto: Gwamna zai fara ba limamai, ladanai da masallatan Juma'a kudin wata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Sokoto zai fara ba limamai alawus

Wannan hari kan sarakuna da limamai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Sokoto ta shirya yi musu gata.

Gwamnatin Sokoto za ta rika biyan alawus ga limamai, na’ibansu da ladanai tare da tallafa wa masallatan Juma’a a duk fadin jihar.

Gwamna Ahmed Aliyu ya ce tallafin kudi daga N300,000 zuwa N500,000 da alawus na wata-wata zai karfafa koyar da addinin Musulunci.

Sarkin Musulmi da sauran shugabanni sun yaba da matakin gwamnati tare da karfafa yara wajen haddar Alkur’ani da zaman lafiya.

Yan Sokoto sun tare hanyoyi kan matsalar tsaro
Taswirar jihar Sokoto da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Sokoto: An yi zanga-zanga bayan sace limamai

Mazauna yankunan suka ce gwamnati ta yi watsi da lamuran tsaro a yankunansu wanda shi ne dalilin zanga-zangar a jihar.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa:

“Rashin kulawar da gwamnati ta nuna mana ya sa muka rufe hanyar mota don janyo hankalinta da jami’an tsaro.
“Yau (Lahadi) sun jera kwana uku kullum sai sun zo sun sace mana mutane kuma babu jami’an tsaro da aka kawo don kare mu.”

Kara karanta wannan

An gudu ba a tsira ba': Sarki ya faɗi yadda mutane 13 suka mutu a kogi a tsarewa yan bindiga

Wata mata mai suna Tunba ta bayyana cewa ta rasa ’ya’yanta guda biyar, ta roƙi gwamnati ta samar musu da tsaro domin su zauna lafiya.

Abin da NEMA, SEMA suka ce kan lamarin

Hukumomin NEMA da SEMA sun ce sun riga sun san da matsalar, inda daruruwan mutane suka tsere daga muhallansu suna neman mafaka a yankin Shagari.

Hakiman kauyukan da abin ya shafa sun tabbatar da hare-haren yayin da suke rokon kawo karshen matsalolin.

Sun roki hukumomin gwamnati ta kawo ɗaukin gaggawa domin jama’a su koma cikin gidajensu lafiya.

A kokarin tsarerwa 'yan bindiga, mutane sun mutu

Mun ba ku labarin cewa wani jirgin ruwa na kwale-kwale ya gamu da hatsari a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma.

Mutanen da ke cikin jrgin kwale-kwalen dai na tserewa 'yan bindiga ne bayan sun hango su suna kusanto inda suke.

Hatsarin ya jawo an rasa rayukan mutane shida har lahira, yayin da wasu kuma aka neme su aka rasa a cikin ruwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.