Magana Ta Kare: Nyesom Wike Ya Bayyana Matsayarsa kan Karawa da Tinubu a 2027
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba saboda yana cikin gwamnatin Bola Tinubu
- Wike ya ce ba zai yi adawa da wanda ya ba shi mukami ba, yana mai jaddada cewa shi d'an halak ne, don haka ba zai yi takara ba
- Ministan ya kuma ce zai ci gaba da zama mai tasiri a PDP ko da kuwa ba shi da kujerar gwamna ko wani mukami a jam'iyyar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba zai tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027 ba, duk kuwa da cewa jam’iyyar PDP ta keɓe tikitin takarar shugaban ƙasa zuwa kudu.
Wike, wanda tsohon gwamnan jihar Ribas ne, ya bayyana haka ne a lokacin tattaunawarsa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin.

Kara karanta wannan
2027: Wike ya kyale Jonathan, ya fadi mutum 1 da zai rusa PDP idan ya samu takara

Source: Twitter
'Ba zan tsaya takara da Tinubu ba' - Wike
Jaridar Punch ta rahoto cewa Wike ya ce ba zai yi takara ba saboda ba ya manta halacci, kuma shi mutum ne mai kare mutuncinsa a siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, ba zai yiwu ya tsaya takara ba a lokacin da shugaban kasa Bola Tinubu, wanda shi ne ya ba shi mukami, ke kan mulki.
"Ba zan yi takara ba. Ina da mutunci, ina da halacci. Babu yadda za a yi, wanda ya ba ni mukami yana kan kujerar, ni kuma in ce zan tsaya takara da shi, ba zai yiwu ba."
- Nyesom Wike.
'Zan ci gaba da yin tasiri a PDP' - Wike
Ministan ya ce ba sai yana rike da mukamin gwamna ba kafin ya taka rawar gani a babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Ya jaddada cewa kasancewarsa cikin jam’iyyar ta taimaka wajen hana ta rushewa gaba ɗaya bayan zaben 2023.
Duk da hakan, Wike ya gargadi PDP cewa babu wata jam’iyyar adawa da za ta tsira idan tana da rikici mai tsanani a cikin gida.
Ya ce babbar matsalar jam’iyyar PDP ita ce rashin iya warware rikicin cikin gida, wanda ke kara raunana ta a idon jama’a.

Source: Facebook
Martanin Wike ga El-Rufai kan tazarcen Tinubu
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, ministan ya kuma karyata ikirarin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, cewa Tinubu zai zo na uku a zaben 2023.
Ya ce lissafi ya kwace wa El-Rufai domin ya gaza bayyana wanda zai zo na farko da na biyu ba kafin ya ce Tinubu zai zo na uku.
Wike ya ce tun kafin zaben 2023 ya yi imani cewa Bola Tinubu ne zai lashe zaɓen shugaban ƙasa, kuma hakan za ta tabbata a 2027.
'Jam'iyyar PDP ba ta koyi darasi ba' - Wike
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Mministan Abuja, Nyesom Wike ya ce har yanzu jam'iyyar PDP ba ta koyi darasi ba, kuma tana shirin tafka kuskure a 2027.

Kara karanta wannan
Ba boye boye: El Rufa'i ya magantu kan zargin muzgunawa Kiristocin Kudancin Kaduna
Nyesom Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake martani game da jita-jitar cewa PDP za ta dawo a Peter Obi jam'iyyar domin ya yi takarar shugaban kasa.
Ministan ya ce idan har PDP ta kuskura ta dawo da Peter Obi, to kuwa ba makawa za ta lalace gaba daya, kuma ta sha kasa a 2027 kamar yadda ta fadi zaben 2023.
Asali: Legit.ng
