NDLEA Ta Kama Tsoho Mai Shekara 70 da Miyagun Kwayoyi, An Lalata Gonar Wiwi
- NDLEA ta kama wani dattijo mai shekaru 70 bisa zargin safarar miyagun kwayoyi da ke kawar da hankalin matasa
- Hukumar ta bayyana cewa ta samu nasara a yakin da ta ke yi da masu safarar migayun kwayoyi a jihohi daban daban
- Ta kara da cewa baya ga cafke tsohon, ta kuma lalata gonar wiwi mai hekta 71.5 a Taraba tare da kama wani matashi dauke da bindiga
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Anambra – Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta kama wani bawan Allah, Uchelue Ikechukwu, a jihar Anambra bisa laifin mallakar miyagun ƙwayoyi.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na NDLEA, Mista Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Source: Facebook
A labarin da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet, ta bayyana cewa Ikechukwu, wanda tsoho ne mai shekaru 70 a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar NDLEA ta yi kame a jihohin Najeriya
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Ikechukwu na daga cikin mutane shida da jami’an hukumar suka kama a wani samame a sassan jihar Anambra.
An cafke shi ne a Umudioka, ƙaramar hukumar Dunukofia, da kilo 26.7 na miyagun kwayoyi da ake sayar wa ga matasa a ranar Alhamis.
Haka kuma, daga cikin sauran mutane biyar da aka kama a tare da shi, an samu da muyagun ƙwayoyi daban-daban a yankunan Nkwelle da Amichi na jihar.
NDLEA ta lalata gonar wiwi a Taraba
A gefe guda, Daraktan yada labarai hukumar, Femi Babafemi ya ce an kuma kama wani matashi mai shekaru 30 a jihar Taraba.
Kamen ya biyo bayan da jami’an NDLEA suka lalata gonar wiwi mai fadin kadada 71.5 a dajin Mayodoga, ƙaramar hukumar Sardauna.
An kama matashin ne da bindiga a ranar 26 ga watan Agusta tare da goyon bayan dakarun Sojojin Najeriya, Hukumar Tsaron Daji da mafarauta.
Babafemi ya bayyana cewa an lalata sama da kilo 178,750 na wiwi a gonar da aka gano a dajin Mayodoga, unguwar Mayosabere, a a karamar hukumar Sardauna.
Jami'an NDLEA sun wayar da kan jama'a
Babafemi ya ƙara da cewa rassan NDLEA da ke fadin kasar nan na ci gaba da shirye-shiryen wayar da kan jama’a cikin shirinta na yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi.
Ya ce sun gudanar da taron ilmantarwa ga ɗaliban sakandare a Onitsha yayin darussan hutun Makarantar Firamare ta Ezechima, Onitsha.
Haka kuma, an wayar da kan matasan cocin Anglican Diocese a Abakaliki, Ebonyi duk domin tabbatar da rage ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Source: Twitter
Sauran wuraren da aka kai ziyara sun haɗa da fadar Sarkin Badagry, HRM De Wheno Aholu Menu-Toyi; MD/CEO na Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta NPA, Dakta Abubakar Dantsoho da tawagarsa a Legas.
Haka kuma, an ziyarci Uwargidan Jihar Ogun, Hajiya Bamidele Abiodun, da kuma Sarkin Isheri, Oba Suleiman Adekunle Bamgbade Ayodele III, da sauran manyan jami’ai.
NDLEA ta yi kame a jihar Kano
A baya, mun wallafa cewa Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta samu nasara a wani samame da ta kai a jihar Kano, inda ta cafke wani matashi.
Mai magana da yawun hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari, ya shaida wa manema labarai cewa jami’an NDLEA sun cafke Adamu Yusuf, bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Maigatari ya bayyana cewa an kama matashin ne a ranar 23 ga watan Agusta, 2025, a Kwanar Dangora, hanyar Zaria–Kano dauke da tramadol 7,000 daga jihar Legas.
Asali: Legit.ng


