An Yi Rashi: Mace Ta Farko da Tinubu Ya Nada Shugabar Ma'aikatan Abuja Ta Rasu

An Yi Rashi: Mace Ta Farko da Tinubu Ya Nada Shugabar Ma'aikatan Abuja Ta Rasu

  • Mace ta farko, kuma 'yar asalin babban birnin tarayya da Shugaba Bola Tinubu ya nada shugabar ma'aikatan hukumar FCTA ta rasu
  • Wata majiya daga hukumar raya babban birnin tarayya (FCTA), ta ce Grace Adayilo ta rasu ne a safiyar Litinin, 1 ga Satumba, 2025
  • A ranar Alhamis din makon jiya ne aka yi wa Grace Adayilo ganin karshe, lokacin da ta wakilci Nyesom Wike a wani taron 'yan G7

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Najeriya ta yi babban rashi yayin da aka sanar da rasuwar Grace Adayilo, mace ta farko da ta zama shugabar ma'aikatan hukumar FCTA.

Mutuwar Grace Adayilo ta girgiza Abuja, da kasar, kasancewar ita ce mace ta farko, kuma 'yar asalin babban birnin tarayyar da ta fara rike wannan mukami.

Grace Adayilo, mace ta farko da ta zama shugabar ma'aikatan FCTA ta rasu
Hoton shugabar ma'aikatan hukumar FCTA, Grace Adayilo da ta rasu. Hoto: @_Mr_Abuja
Source: Twitter

Shugabar ma'aikatan Abuja ta rasu

Kara karanta wannan

MURIC ta kausasa harshe kan kisan matar da ake zargi da kalaman batanci a Neja

Wata majiya daga hukumar raya birnin tarayya (FCTA), ta tabbatar da cewa Grace ta mutu ne a safiyar ranar Litinin, 1 ga Satumbar 2025, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoton, babu wata sanarwa da iyalanta ko gwamnatin FCTA suka fitar game da mutuwar Grace.

An ji cewa lokacin karshe da aka ga Grace shi ne a ranar Alhamis din makon jiya, inda ta wakilci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike a taron G7 a Abuja.

Tinubu ya nada shugabar ma'aikatan FCTA

A watan Oktoba, 2024 ne Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Grace Adayilo matsayin mace ta farko, kuma 'yar asalin Abuja, matsayin shugabanar ma'aikatan FCTA.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa nadin Grace ya zama wani tarihi a babban birnin tarayya, kuma ya karya duk wani shinge na banbancin jinsi.

An ce nadin ya yi daidai da shirin Shugaba Tinubu ta Renewed Hope, wanda ke da nufin samar da wakilci a gwamnati ba tare da wariyar jinsi ko kabilanci ba.

A lokacin, shugaban kasar ya ce nadin Grace zai fara aiki nan take, inda ta maye gurbin Dr. Atang Udo Samuel.

Kara karanta wannan

NDLEA ta kama tsoho mai shekara 70 da miyagun kwayoyi, an lalata gonar wiwi

An ce Shugaba Tinubu ne ya nada Grace matsayin shugabar ma'aikatan FCTA a Oktoba, 2024.
Tambarin hukumar babban birnin tarayya Abuja. Hoto: @OfficialFCTA
Source: Twitter

Burin shugabar ma'aikatan FCTA da ta rasu

Gwamnatin tarayya ta yi fatan cewa shugabancin Grace zai taka muhimmiyar rawa wajen karfafa tsarin gudanar da FCTA tare da inganta ayyukan gwamnati.

A ranar 5 ga Oktoba, 2024, lokacin da ta shiga ofis, Grace ta ce:

“Na gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ministan Abuja, Barista Ezenwo Nyesom Wike. Na yi alkawarin bin tafarkin Renewed Hope na shugaban kasa, tare da sauke nauyin da aka dora mun.”

Kafin nadinta, Adayilo ta yi aiki a matsayin babbar kwamishiniya ta ma’aikatar noma da cigaban karkara, inda ta ta yi amfani da kwarewarta wajen tafiyar da aikin da aka ba ta.

FCTA ta kwace motocin mutane a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar FCTA ta sanar da cewa ta kwace akalla motoci 700 saboda amfani da lambar mota ta jabu da gilashi mai duhu.

Hukumar raya Abujan ta ce mafi akasarin masu fashi da makami a kan hanyoyin birnin da ake kira one-chance na amfani da gilashi mai duhu.

A yanzu dai hukumar FCTA ta bayyana cewa shirinta na "Tsaftace Abuja" ya rage fashin one-chance yayin da aka gargadi direbobi kan karya dokokin tuki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com