Ba Boye Boye: El Rufa'i Ya Magantu kan Zargin Muzgunawa Kiristocin Kudancin Kaduna

Ba Boye Boye: El Rufa'i Ya Magantu kan Zargin Muzgunawa Kiristocin Kudancin Kaduna

  • Tsohon gwaman jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce kalaman da ake yi masa na cewa mai tsattsauran ra’ayi ne ba gaskiya ba ne
  • Ya bayyana cewa ba ya damuwa da sukar makiya, domin bai dogara da ra’ayinsu wajen tafiyar da rayuwarsa ba
  • Tsohon gwamnan ya ce a lokacin mulkinsa a jihar Kaduna ya yi aiki da kowa ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce bai damu da abin da makiya ko masu adawa da shi ke tunani a kansa ba.

Ya bayyana haka ne ya yi da aka tambaye shi game tunanin da wasu ke yi da ya kai ga kiran shi da mai tsattsauran ra’ayi.

Kara karanta wannan

'Ban taba abokantaka da Uba ba,' El Rufa'i ya fadi alakarsa da gwamnan Kaduna

Tsohon gwamnan Kaduna, El Rufa'i yana jawabi a wani taro
Tsohon gwamnan Kaduna, El Rufa'i yana jawabi a wani taro. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Twitter

El-Rufai ya bayyana haka ne a cikin wani shirin Channels Television, inda ya ce yawancin wadanda ke tsangwamar sa ba su taba haduwa da shi ko yin aiki da shi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ban damu da sukar makiya ba,” El-Rufa'i

A cewar Nasir El-Rufai, makiyansa sun fi tsananin kiyayya ne saboda bai taba damuwa da tunaninsu ba.

Daily Post ta wallafa cewa ya ce:

“Ban damu ba. Wadanda ke cewa ni mai tsattsauran ra’ayi ne ba su san ni ba, ba su taba yin aiki da ni ba.
"Dalilin da yasa makiya ke tsananin kiyayya da ni shi ne saboda ba na damuwa da abin da suke tunani.”

Ya bayyana cewa ya ji daɗin yadda ya tafiyar da rayuwarsa ta mulki, kuma wadanda suka taba aiki tare da shi sun san yadda yake.

Martani kan zarge-zargen Kudancin Kaduna

Da aka tambaye shi kan zargin cewa ya nuna wariya a wasu sassan Kudancin Kaduna a lokacin mulkinsa, El-Rufai ya karyata hakan.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: El Rufai ya fallasa abin da gwamnatin Tinubu ke yi wa 'yan bindiga

Ya ce:

“Su na iya tunanin abin da suke so, amma ni ban dauki raini ba. Mulki ba wasa ba ne. Idan kana mulkin mutane miliyan 10, ba za ka nuna bambanci tsakanin wannan da wancan ba.”

El-Rufai ya ce akwai mutanen Kudancin Kaduna da suka ji tamkar suna da gata na yin abin da suka ga dama, amma gwamnatinsa ta yi aiki bisa doka tare da kowa.

Ya kara da cewa daga cikin wadanda ya fi kusanci da su a gwamnati akwai wadanda suka fito daga yankin Kudancin Kaduna.

Tsohon gwamnan ya ce idan aka yi dubi da abin da ya faru tsakaninsa da 'yan Shi'a da suke addini daya da shi, za a fahimci cewa ba nufin muzgunawa Kiristoci ya yi a Kudancin Kaduna ba.

El-Rufa'i yayin wani taron ADC a Kaduna
El-Rufa'i yayin wani taron ADC a Kaduna. Hoto: ADC Vanguard
Source: Facebook

Maganar rage barnar kudi a Kaduna

Tsohon gwamnan ya ce a lokacin mulkinsa ya dauki matakai da dama domin dakatar da dabi’un da ba su dace ba a gwamnati.

Kara karanta wannan

'Ba don addini ba ne,' El Rufa'i ya fadi dalilin kawo tikitin Muslim Muslim a 2023

El-Rufa'i ya bayyana cewa ya yi kokarin rage kashe kudin gwamnati a wuraren da ba su da amfani.

Ya bayyana cewa dattawan Kudancin Kaduna sun taba neman karin mukamai da kuma wasu tallafi daga gwamnati, amma ya ki amincewa.

Babban 'dan adawar ya zargi PDP da amfani da kuri'un yankin wajen murde zaben Kaduna a baya, don haka aka rika ba su mukamai rututu.

El-Rufa'i: Dalilin kawo tikitin Muslim Muslim

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce sun kawo Muslim Muslim ne domin cimma manufar siyasa.

Tsohon gwamnan ya ce saboda haka ne ma za a ga ba wanda aka nuna wa wariya a lokacin da ya ke gwamna karkashin Muslim Muslim.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shettima ne suka tsaya karkashin tikitin Muslim Muslim a zaben 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng