Za a Dauki Matasa 400,000 a Shirin YouthCred, Kowane na Iya Samun N200,000 a Najeriya
- Shirye-shiryen bayar da rance ga matasan Najeriya karkashin shirin YouthCred ya kankama bayan kaddamar da shi karo na biyu a jihar Legas
- Ministan harkokin matasa, Ayodele Olawande ya ce shirin zai bai wa matasa akalla 400,000 rancen kudi, wanda ka iya kai wa N200,000
- Ya ce shirin ya kunshi matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) da sauran yan Najeriya a jihohi 36 da birnin tarayya Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da shirye-shiryen fara aiwatar da shirin bai wa matasa rance na YouthCred.
Shirin dai na daya daga cikin manufofin ajendar Renewed Hope ta Shugaba Tonubu domin tallafawa matasa su samu abin dogaro da kai a fadin Najeriya.

Source: Twitter
The Nation taruwaito cewa bayan kaddamar da shirin a Abuja kwanakin baya, Gwamnatin Tinubu ta sake shirya taro kan tsarin bayar da rance ga matasan a Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron ya gudana ne a sansanin bai wa matasa yan bautar kasa (NYSC) horo da ke Ipaja a jihar Legas, bayan kaddamar da shi tun farko a sasanin NYSC da ke Kubwa a Abuja.
Ministan harkokin matasa, Kwamared Ayodele Olawande da shugaban shirin ba da lamuni na CREDICORP, Uzoma Nwagba da wasu masu ruwa da tsaki ne suka jagoranci taron.
An tsara bai wa matasa 400,000 rancen kudi
A cewar masu shirya taron, YouthCred shiri ne na ba da lamuni, wanda zai samar da bashi mai inganci, gaskiya, sassauci da araha ga matasa fiye da 400,000, ciki har da ‘yan NYSC.
Yayin taron, wanda dubban matasa suka halarta, Ministan Matasan, Olawande, ya bayyana cewa shirin ba na ‘yan bautar ƙasa kaɗai ba ne, kowane matashi zai iya nema ya samu.
A nasa jawabin, Shugaban CREDICORP, Injiniya Nwagba, ya bayyana shirin a matsayin wani juyin juya hali da zai fara gina al’adar amfani da rance a Najeriya.

Kara karanta wannan
Tinubu ya hada kai da kungiyar kasashen musulmi, za a tallafawa mata miliyan 10 a Najeriya
Shugaba Tinubu zai inganta harkokin matasa
Ya ce Shugaba Tinubu yana da hangen nesa mai kyau ga matasan ƙasar, kuma CREDICORP wani ɓangare ne na taimaka musu su ƙarfafa kansu, rahoton The Cable
Ya ƙara da cewa shirin YouthCred ba wai rance kaɗai ba ne, wani yunkuri ne da ke ƙoƙarin sauya tunanin matasa kan kuɗi, aro, amana da ɗaukar nauyin kuɗi cikin gaskiya.

Source: Twitter
Yayin da yake tuna yadda ya yi bautar ƙasa a sansanin Ipaja shekaru 15 da suka wuce, Nwagba ya ce karbar bashi a wancan lokaci shi ne ya taimaka masa wajen ci gaba da rayuwa.
Gwamnatin Tinubu za ta horar da matasa miliyan 7
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya kawo shirin da za a dauki matasa miliyan bakwai domin horar da su kan fasahar zamani a fadin Najeriya.
Matasan da za su ci gajiyar wannan shiri za su samu horo da gogewa a fannoni kamar fasahar AI, tsaro na yanar gizo da kuma kirkiro manhajar kwamfuta.
Gwamnatin tarayya ta ce matasa suna taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasa kuma wajibi ne a ba su horon abubuwan zamani, dabi’u da tunani domin su ne shugabannin gobe.
Asali: Legit.ng
