Lahadi: Ruwan Sama da Iska Mai Ƙarfi Zai Sauka a Abuja, Neja, Yobe da Wasu Jihohi

Lahadi: Ruwan Sama da Iska Mai Ƙarfi Zai Sauka a Abuja, Neja, Yobe da Wasu Jihohi

  • NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai yawa zai sauka a jihohin Arewa maso Yamma, maso Gabas da Tsakiya
  • Jihohin Arewa sa ake sa ran za su samu ruwan a yau Lahadi, 31 ga Agusta, 2025 sun hada da Yobe, Neja, Zamfara
  • NiMet ta gargadi al’umma kan hadurran da iska da ambaliya za su iya jawowa, tare da ba da muhimman shawarwari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da hasashen yanayi ta ƙasa (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai yawa a ranar Lahadi.

NiMet ta bayyana cewa, ruwan sama zai sauka da tsawa da kuma iska mai karfi a sassa daban-daban na Najeriya a yau, 31 ga Agusta, 2025.

Hukumar NiMet ta ce za a samu ruwan sama mai yawa a Neja da wasu jihohin Arewa a ranar Lahadi
Ruwan sama mai ƙarfi tare da tsawa na sauka aga sararin samaniya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

NiMet ta bayyana hakan ne a cikin jadawalin yanayi da ta fitar a ranar Asabar, a shafinta na X, kamar yadda Legit Hausa ta gani.

Kara karanta wannan

'Na shirya rungumar zaman lafiya': Bello Turji ya dauki alkawari, ya fadi sharrin da ake yi masa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen yanayi a Arewacin Najeriya

Rahoton ya nuna cewa lamarin zai fi yin tasiri musamman a Arewa maso Yamma, maso Gabas da Tsakiyar ƙasar nan, tare da wasu jihohin Kudu.

A Arewa, jihohin Kebbi, Zamfara, Katsina, Borno, Yobe da Taraba za su fuskanci ruwan sama mai tafiya da tsawa da iska mai karfi a safiyar Lahadi.

Rahoton ya ƙara da cewa a yammacin yau ma, mafi yawan sassan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas za su ci gaba da fuskantar irin wannan yanayi.

A Arewa ta Tsakiya kuwa, ana sa ran za a yi ruwan sama kaɗan a wasu sassan jihar Benue da safe, kafin daga baya ya tsananta a jihohin Nasarawa, Kwara, Niger, Plateau, Kogi da babban birnin tarayya Abuja.

Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya

A Kudu kuma, NiMet ta ce za a wayi gari da gajimare a jihohin Cross River da Akwa Ibom, inda ake sa ran ruwan sama kaɗan.

Kara karanta wannan

NiMet ta yi hasashen ruwa da guguwa a Kano, Gombe da wasu jihohin Arewa

Sai dai daga bisani a yammacin yau, ana hasashen ruwan sama a Lagos, Ondo, Edo, Abia, Imo, Ebonyi, Ogun, Cross River, Akwa Ibom, Delta, Rivers da Bayelsa.

Hukumar NiMet ta shawarci mazauna garuruwan da ke fuskantar ambaliya su shirya.
Jami'an hukumar NiMet na duba na'urar hasashen yanayi a Abuja. Hoto: @nimetnigeria
Source: Twitter

NiMet ta gargadi ƴan Najeriya

Hukumar ta yi gargadin cewa ruwan sama mai hade da tsawa da iska mai karfi kan iya jawo hadurra, sannan ƙauyuka masu fama da ambaliya na iya shiga cikin tashin hankali.

“Al’umma su yi hattara da iska mai karfi da ke tare da ruwan sama. Mazauna wuraren da ake fama da ambaliya su kasance cikin shiri a kowane lokaci,” inji sanarwar NiMet.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da sa ido kan yanayi tare da bayar da rahotanni lokaci-lokaci domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Domin neman karin bayani, NiMet ta ce a ziyarci shafukanta na sada zumunta, ko kuma a shafin yanar gizon hukumar: www.nimet.gov.ng.

Ambaliya: China ta ba Najeriya tallafin N1.5bn

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Najeriya ta kulla yarjejeniya da China domin bayar da tallafin Dala miliyan 1 ga mutanen da ambaliya ta shafa a Arewa.

Kara karanta wannan

Borno: Mayakan boko haram sun yi wa matafiya kwantan bauna, sun bude wa motarsu wuta

Ministan Tsare-tsare da Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, ya bayyana tallafin a matsayin taimakon gaggawa da zai saukaka radadin rayuwa.

Hukumar SEMA a Jihar Yobe ta fara kwashe iyalai sama da 250 daga Garin Kolo zuwa wasu wurare domin kare su daga sake fadawa cikin ambaliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com