An Gudu ba a Tsira ba': Sarki Ya Faɗi yadda Mutane 13 Suka Mutu a Kogi a Tsarewa Yan Bindiga

An Gudu ba a Tsira ba': Sarki Ya Faɗi yadda Mutane 13 Suka Mutu a Kogi a Tsarewa Yan Bindiga

  • Mutane da dama sun rasa rayukansu a kokarin tserewa yan bindiga da suka kawo wani hari a jihar Zamfara
  • An tabbatar da cewa mutum 13 sun nutse a kogi a Birnin Magaji da ke jihar Zamfara lokacin da maharan suka kawo hari
  • Rahotanni sun nuna cewa kwale-kwale guda daya kawai aka samu, wanda ya cika da jama’a, hakan ya janyo hatsarin da ya hallaka mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin Magaji, Zamfara - Hakimin Birnin Magaji a jihar Zamfara ya tabbatar da mutuwar mutane har guda 13 a yau Asabar.

Basaraken ya ce mutane sama da 13 sun mutu a cikin wani kogi a lokacin da suke kokarin tserewa daga harin ‘yan bindiga a Birnin Magaji a jihar Zamfara.

Mutane 13 sun mutu a Zamfara a harin yan bindiga
Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Yan bindiga: Mutane 13 sun mutu a kogi

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sha wuta hannun sojojin sama, sun sako mutanen da suka sace a Zamfara

Rahoton TheCable ya ce yan bindiga sun kai farmaki kan wasu kauyuka biyu a Birnin Magaji ranar Juma’a, lamarin da ya sa mazauna garin suka nemi hanyar tsira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin guduwa, wasu daga cikin mazauna yankin suka isa bakin kogi domin shiga jirgin ruwa guda daya da aka samu don tsallakawa zuwa daya gefen kogi.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya cika da jama’a sosai, wanda ya janyo ya nutse yayin tafiya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane.

Yadda uba ya rasa ƴaƴansa a jihar Zamfara

Shehu Mohammed, wani ma’aikacin lafiya a Birnin Magaji, ya ce babban ɗansa da ‘yan uwansa biyu sun mutu cikin hadarin kwale-kwalen.

“Babban ɗana da wasu yan uwansa guda biyu suna daga cikin mutane 13 da suka mutu bayan kwale-kwale ya kife da su."
Sarki a Zamfara ya koka da harin yan bindiga
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Basarake ya fadi yadda abin ya faru

Hakimin Birnin Magaji, Maidamma Dankilo ya tabbatar da haka inda ya ce an ceto mutum 22, yayin da har yanzu 22 suke bace, Punch ta ruwaito.

A ‘yan kwanakin nan, hare-haren ‘yan bindiga sun karu a Zamfara, inda ake kashe mutane, yin garkuwa da kuma lalata rayuwar al’ummomin kauyuka.

Kara karanta wannan

A karo na 3, jirgi ya gamu da hatsari mai muni a jihar Sokoto, mutane da dama sun mutu

A makon da ya gabata, ‘yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da sace akalla 100 a Gamdum Mallam da Ruwan Rana na Bukkuyum.

Zamfara: Hare-haren yan bindiga a kwanakin nan

A farkon watan Agusta, maharan sun kutsa kauyuka da dama a Kauran Namoda inda suka kashe mutum 24, suka raunata 16, suka sace 144 yayin harin.

A watan Yulin 2025 da ta gabata kuwa, rahotanni suka bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum 33 a Banga bayan karɓar kudin fansa na Naira miliyan 50.

Yan bindiga sun sha wuta a Zamfara

Kun ji cewa dakarun sojoji na ci gaba da kokarin ganin an samu tsaro a jihar Zamfara wadda ke fama da matsalar 'yan bindiga.

Sojojin sama na rundunar Operation Fansan Yanma sun kai dauki bayan da 'yan bindiga suka yi awon gaba da mutane masu yawa a kauyuka.

Ruwan wutan da jiragen sojojin saman suka yi wa 'yan bindigan, ya tilasta musu tserewa domin tsira da rayukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.